Shin Rasha na da tasiri ga nahiyar Afirka?

A wannan makon ne Rasha ta karbi bakuncin shugabannin Afirka, abun da ke nuna irin muhimmiyar gudummawar da kasar ke bai wa nahiyar.

A baya tarayyar Soviet na da tasiri a yankin na Afirka, sai dai irin tasirin da kasar ke da shi ta fannin siyasa da tattalin arziki a yankin ya ragu tun bayan yakin basasa.

Shugaba Vladmir Putin ya ce inganta alakar da ke tsakanin Rasha da kasashen Afirka na daya daga cikin tsare-tsaren da kasarsa ta bai wa mahimmanci.

Wata tawagar BBC ta musamman ta yi nazari kan ko menene mahimmancin Rasha a Afirka?

Mene ne kudirin Rasha?

Ya bayyana cewa Moscow tana ganin kasancewarta a nahiyar Afirka a bangarori da dama na inganta alakar.

Cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai, TASS gabanin taron na wannan makon, shugaba Putin ya ce alakar Rasha da Afirka tana da mahimmanci sannan ya yi magana kan abubuwa kamar haka:

  • Tallafa wa fannin siyasa da diplomasiyya
  • Bayar da taimako a bangaren tsaro
  • Habaka tattalin arziki
  • Bayar da shawara kan dakile cututtuka
  • Bayar da taimakon kayayyakin agaji
  • Horarwa ta fannin ilimi da sana'oi

Rasha dai na kara habaka alakar siyasa a yankin inda shugabannin Afrika 12 suka ziyarci Rashar tun shekarar 2015 - a cikin shekarar 2018 kadai, shugabannin Afirka 6 ne suka je Rasha.

Sai dai kudurorin da Rasha ke da su yasa wasu mahimman kasashen yamma daga murya cewa Rashar na neman wuce gona da iri.

Ko a shekarar da ta gabata, tsohon mashawarcin Shugaban Amurka kan harkokin tsaro, John Bolton, ya sanar da wata sabuwar dabara da za ta rushe kusancin da Rasha da China ke da shi ga Afirka.

Ko da ya ke wani rahoto da aka wallafa a jaridar Washington Post, ya yi bayani kan yadda Rasha ke neman kulla alakar tsaro ta ko wane hali da Afirka yayin da tasirin da Amurka ke da shi a nahiyar ke ci gaba da disashewa.

Alakar Rasha da Afirka ta fuskar tsaro

Rasha wata babbar kawace ga Afirka ta fannin tsaro kuma ita ce kasar da take samar wa yankin makamai.

Sai dai a duniya, Afirka ba ita ce nahiyar da ta fi cin gajiyar makamanta ba.

Tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018, kasashen nahiyar Afirka (ban da Masar) su ne suke da kashi 17 cikin 100 na makaman da Rasha ke fitarwa zuwa wasu kasashen kamar yadda cibiyar nazari kan zaman lafiya ta duniya, Stockholm International Peace Research Institute (SIPRI) ta bayyana.

Daga cikin abubuwan da Rashar ke fitarwa, kashi mafi tsoka na zuwa ne Algeria yayin da sauran kasashen ke tashi da kasa da kashi uku cikin dari na jimillar kayayyakin da Rashar ke fitarwa.

Hakan na nufin yawan makaman da kasashen Kudu da Sahara ke samu basu taka kara sun karya ba.

Sai dai kuma alakarsu ta fuskar tsaro na ci gaba da habaka, kuma tun shekarar 2014, akwai yarjejeniyoyi kan tsaro da suka kulla da wasu kasashen Afirka 19.

A shekarar 2017 zuwa 2018, Rasha ta kulla kawancen samar da makamai ga kasashen Angola da Najeriya da Sudan da Mali da Burkina Faso da kuma Equatorial Guinea, makaman da suka hada da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu da tankokin yaki da kuma injinan jiragen yaki.

Amfani da kwararrun jami'an tsaro

Kawancen Rasha ta fuskar tsaro ya wuce kawai samar da makaman yaki ga wasu kasashen, har ma a wasu lokutan ta hada da yin amfani da kungiyoyin tsaro masu zaman kansu.

Misali, Rasha ta kasance a jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya, inda ta ke tallafawa kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Amma dakarun da ba na gwamnatin Rasha ba ne suma suna aiki a kasar, inda suke samar da tsaro ga gwamnati da kuma taimaka wa wajen tsare tattalin arzikinta.

Kazalika irin wadannan dakaru na aiki a Sudan da Libya da ma wasu kasashen, har da wani kamfani mai zaman kansa mai suna Wagner da ya kulla kawance da Abuja.

Jami'an Rasha dai basu cika bai wa irin wadannan rahotannin mahimmanci ba, sannan abu ne mai wuya a iya gano alakarsu da Rasha da kuma irin goyon bayan da suke da shi wajen gudanar da harkokinsu.

Sai dai Paul Stronski, babban jami'i a wata cibiyar samar da tsaro ta duniya da ke Amurka na ganin, wadannan jami'an tsaron masu zaman kansu na amfanar Rashar.

Suna samar wa kansu kudade ta hanyar ayyukansu, sannan suna bai wa Rasha damar fadada jami'an tsaro da tasirin da take da shi ta fannin siyasa a kasar a kyauta.

Albarkatun Kasa

Rasha dai na samun tagomashi kan sanya kanta a harkokin Afirka, ganin cewa tana da karancin albarkatun kasa kamar sinadaran Magnese da bauxite da chromium, wadanda suke da mahimmanci ga tsaro.

Tana kuma da kwarewa a bangaren makamashi da za ta ita yi wa kasashen da ke da albarkatun kasa tayi.

Kamfanoni mallakin Rasha suna hakon Bauxite a kasar Guinea, inda suke kulla yarjeniyoyi tare da samun damar samar da iskar gas a Mozambique.

An rawaito babban kamfanin sarrafa makamashi na Lukoil yana aiki a Kamaru da Ghana da kuma Najeriya, sannan yana duba yiyuwar samun dama a jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Rasha dai na yi wa kasashen Afirka da dama tayin fasahar kera makaman nukiliya har da tayin gina makeken wajen hada makamashin nukiliya a Masar, wanda za a gina da rancen dalar Amurka biliyan 25 da aka samu.

Amma kuma, Rasha ta fi yin alakar kasuwanci da nahiyar Turai da Asia idan aka kwatanta da yadda take yi da Afirka.

Sannan kasashen Kudu da Sahara sun fi yin huldar kasuwanci da India a shekarar 2017 da China da Turai da kuma Amurka ban da Rasha.

Kazalika, Amurka da China da Japan da Turai sun fi bai wa yankin Afirka tallafi wajen samar da ci gaba da zuba hannun jari a yankin idan aka kwatanta da Rasha.

Sai dai duk da cewa Rasha tana aiki wajen daga darajarta da inganta alakarta da Afirka, tana da sauran aiki a gaba, idan tana so ta kamo sauran kasashen duniya.