Ko namiji zai iya shan kwayoyi domin tazarar haihuwa?

    • Marubuci, Daga Farfesa Lisa Campo-Engelstein
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Albany Medical College

Masana kimiyya sun kwashe tsawon shekara hamsin suna aiki kan samar da kwayar maganin tazarar haihuwa ta maza.

Sai dai duk da rahotanni da ke kara karfafa gwiwa kan hakan, ba kwanan nan za a fara samun maganin a shaguna ba.

Rashin kudi da rashin sha'awar shan maganin da ake tunani mazan na da shi, na nufin har yanzu ba a taba hada kwayoyin masu yawan gaske ba. Amma, har yanzu ana daura laifin rashin daukar ciki a kan mata.

Koda yake bincike ya nuna cewa maza da yawa za su sha magnanin idan aka samar da shi.

Kashi uku na mazan Burtaniya masu jima'i sun ce za suna iya amfani da kwayoyin tazarar haihuwa. Wannan kuma ya zo dai-dai da adadin matan Burtaniya da ke shan irin wadannan kwayoyin.

Mutum 8 cikin mutum 10 a binciken sun ce kamata ya yi a raba shan kwayoyin tsakanin ma'aurata biyu.

Sai dai, kashi 77 cikin dari na maza masu jima'i a Amurka da ke tsakanin shekara 18 zuwa 44 da aka yi binciken a kansu sun ce, suna tunanin watakila su gwada amfani da kwayoyin a maimakon kwaroron roba da dandaka.

To ko samun karbuwa daga wurin mutane da kuma sassauta dokokin zamantakewar aure, za su iya sanya wa a samar da kwayoyin tazarar haihuwa na maza?

To me yasa har yanzu ba a yi maganin ga maza ba?

An fara samar da maganin hana daukar ciki ga mata bayan shekara goma da kirkiro shi.

Amma me yasa aka dauki dogon lokaci babu kwayar maganin na maza a kasuwa.

Wasu masana kimiyya sun ce kirkiro kwayoyin hana yin ciki na maza ya fi sarkakiya ne a kan na mata.

Kwayoyin mazan dai na dakatar da zuwan ruwan maniyyi ga namiji, sai dai yawan kwayoyin halittar da ake son su yi hakan za su janyo wata matsalar ta daban.

Haka kuma akwai wasu dalilai masu nasaba da rayuwar yau da kullum da kuma na tattalin arziki.

Hakazalika fannin yaduwar al'umma ya fi mayar da hankali ne a kan jikin mata fiye da maza. Alal misali kusan ace kowa ya san aikin kwararren likitan mata, sai dai watakila mutane kalilan ne suka san aikin kwararraen likitan maza, wanda likita ne da ya kware kan abubuwan da suka shafi haihuwa ga namiji.

Bugu da kari kuma rashin isassun kudade ya taimaka wajen daukar lokaci kafin a samar da magunguna na maza, duk kuwa da cewa an fara bincike a kansa dab da fara samar da na mata.

Wasu dalilan da suka janyo hakan sun hada da cewa kamfanonin samar da magunguna da hukumomin da ake sa ido da kuma su kansu mazan da alamu ba su shirya amincewa da matsalolin da magungunan ka iya janyowa.

Yayin da aka amince da irin matsalolin da mata kan samu a sanadiyyar shan maganin hana haihuwar, saboda ana auna irin hatsarinsa da na juna biyu. Yayin da su kuma maza a nasu bangaren ana auna nasu.

Haka kuma, matsalolin da aka saba samu a magungunan matan kamar yin kiba, sauyin yanayin mutum da kuma rashin sha'awar yin jima'i ana kallonsu tamkar ragewa maza kimarsu ne.