'Yadda na tsani kowa har mijina bayan na haihu'

Bayanan bidiyo, Alamomin cutar tsananin damuwa bayan haihuwa
    • Marubuci, Fauziyya Kabir Tukur
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Karima (ba sunanta na gaskiya ba) ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na tsananin bakin ciki da damuwa da fargaba wanda ba ta taba tunanin dan Adam na iya shiga ya wanye lafiya ba.

Kamar kowa ce mace mai ciki, Karima ta yi farin ciki a lokacin da ta fahimci tana dauke da juna biyu, inda ta fara shirye-shiryen tarbar jaririyarta cikin doki da zakuwa.

Sai dai da lokacin haihuwarta ya yi, sai likitoci suka ce mata ba za su bari ta haihu da kanta ba sai dai su yi mata tiyata saboda dalilai masu karfi.

Karima ta bayyana cewa ba ta taba tunanin haihuwar za ta zo mata da wata matsala ba amma likitocinta sun nuna mata yin tiyatar shi zai fi.

Ita da maigidanta suka amince da wannan shawara, aka sa ranar da za ta je asibiti domin yin aikin.

A lokacin da za ayi tiyatar, sai likitoci suka yi mata allurar kashe zafi mai karfi, wato anaesthesia da Ingilishi, wadda za ta ba su damar yanka cikin Karima ba tare da sun sa ta bacci ba kuma su ciro jaririyar ba tare da ta ji zafi ba.

Dan lokaci bayan yi mata wannan allurar, sai Karima ta fara jijjiga, alamun jikinta bai amince da allurar ba.

Nan da nan likitocin suka yi mata wata allurar da ta sa ta bacci mai nauyin gaske.

Ashe wasa farin girki a matsalolin da suka dabaibaye haihuwar Karima.

Yin allurar baccin ke da wuya jini ya balle mata, don haka dole likitocin suka shiga aiki tukuru don kokarin ceto ranta.

"Likitocin kansu sun yi tunanin mutuwa zan yi saboda matsalolin da suka rika tasowa bi da bi," in ji Karima.

Amma an yi nasarar ceto ta, kuma an ciro jaririya mai koshin lafiya.

Wanshekare, ko da Karima ta tashi daga bacci sai ta fahimci cewa ba ta iya magana sai da kyar da sidin goshi kalma daya za ta fita daga bakinta.

Post-Partum Depression

Asalin hoton, Getty Images

Karima ta ce "Kamar a fim, kafin kalma daya ta fita daga bakina sai na tattaro numfashi da kyar, na rika haki.

"Sai da aka rubuta min wasu magunguna na fara sha sannan na fara samun sauki. Ashe allurar baccin nan da aka yi min ce ta jawo min daukewar numfashin saboda jikina ba ya sonta."

'Kamar an sa ni a daki mai duhu'

Karima ta ce bayan ta farfado daga baccin, ta yi matukar farin cikin ganin jaririyarta fiye da yadda take tsammani kuma ta ji ba ta so a matsa da ita ko nan da can.

Amma kan a je ko ina sai ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na tsananin bakin ciki da bata taba jin irinsa ba, amma wannan bai hana ta matse jaririyarta a jikinta ba.

Sai dai ta ji ta tsani ganin mutane a kusa da ita gaba daya.

"Na ji bana son ganin kowa. Na kira likita na ce masa ya hana baki shigowa dakin da na ke, na ce su rubuta a jikin kofar dakina cewar an hana baki shiga."

Karima ta ce kawai sai ta fara tunanin yadda za ta gudu saboda tsananin bacin ran da take ciki, bacin ran da ba ta san abinda ya haifar mata da shi ba.

"Na shaida wa mahaifiyata da ke zaune da ni a asibiti cewa da an sallame mu daga asibiti zan gudu in bar nan ni da jaririyata.

"A yanzu idan na tuna na kan yi dariya amma a lokacin da gaske na yi wannan shirin.

"Bakin ciki ne da ba ya misaltuwa, na ji kamar an sa ni a wani daki mai matukar duhu."

Karima ta ce mahaifiyarta ce ta rika tarairayarta tare da ba ta baki, har aka sallamesu suka koma gida.

Sai dai bata samu sassaucin wannan bakin ciki da ta tsinci kanta a ciki ba har bayan da ta koma gida.

'Ba na iya bacci sai na rike jaririyata'

"Wata rana, mahiafiyata ta shigo daki ta samu na dora jaririyata a kan kirjina, haka ya zama abin da nake yi kullum. Idan ban dora ta a kirjina na rike ta ba, bana iya bacci.

"Hawaye na ta gangarowa daga idanuna, kuma nima kaina ban san dalilin kukan ba gaskiya."

Mother and child

Asalin hoton, Getty Images

Karima ta ce mahaifiyarta ta zamo mata abin dogaro, don ita kadai ce ta fahimci halin da take ciki kuma take jurewa ta ba ta baki.

"Maigidana bai fahimci abin da ke faruwa da ni ba, don haka bai san ta wace hanya zai bullo min ba.

"Bai san irin halin matukar takaicin babu gairi babu dalili da nake ciki ba, sai da ta kai ba ma yi wa juna magana. Idan ya ce abu fari ne sai in dage in ce a'a baki ne," ta bayyana tana dariya.

"Idan ina tuna wannan lokacin ni kaina ina mamakin yadda na rika mu'amala da shi. Sai da ta kai mun daina magana da juna sai dai mu aika wa juna sako ta manhajar Whatsapp." in ji Karima.

Cutar tsananin damuwa bayan haihuwa

Cutar tsananin damuwa bayan haihuwa ciwo ne da kan samu iyaye mata bayan haihuwa.

Ana yawan samun mata masu kamuwa da wannan ciwo sai dai ba su cika fada ba, kuma da wuya su je asibiti.

An gudanar da wani bincike a jami'ar Jos da ke yankin tsakiyar Najeriya inda aka duba sabbin iyaye mata 392.

Binciken ya gano cewa kashi 55 cikin 100 na wadannan mata na fuskantar wasu alamu na wannan cutar, kuma tana da alaka da tunanin kashe kai.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kusan kashi 10 cikin 100 na mata masu ciki da kashi 13 cikin 100 na matan da basu dade da haihuwa ba na fuskantar rashin lafiyar kwakwalwa, musamman ma cutar tsananin damuwa.

Yagana Gambo- Dauda wata kwararriya ce kan lafiyar kwakwalwa kuma ta bayyana cewa cutar tsananin damuwa bayan haihuwa na faruwa ne idan wasu sinadarai a kwakwalwar uwa suka sauya.

"Wani lokaci kuma sauye-sauyen da kan zo a lokacin haihuwa ko bayan haihuwa kan haifar wa uwa wannan cuta," in ji Yagana.

Ta ce wani lokaci, sabbin iyaye mata kan fuskanci gajiya ko saurin hushi da dai sauransu idan sun haihu kuma wannan ba abin damuwa bane.

Amma tsananin fushi da bakin ciki da tsanar rayuwa manyan alamomi ne na cewa uwa ba ta da lafiya.

Mene ne alamomin cutar?

Yagana Gambo- Dauda ta ce alamominta na da yawa amma manyan alamominta sun hada da:

  • Rashin son cin abinci
  • Tsananin bacin rai
  • Kuka babu gaira babu dalili na tsawon lokaci
  • Rashin son mutane, ko da 'yan uwanta ne
  • Rashin bacci ko kuma yawan bacci
  • Yawan gajiya
  • Daina sha'awar yin abubuwan da a baya take son yi
  • Tunanin kashe kanta
  • Rashin shakuwa tsakanin uwa da jaririnta
  • Rashin mayar da hankali wajen son a shaku da jariri

Ya ake gano cutar?

Yagana Gambo- Dauda ta ce gano cutar ba shi da wahala amma likita zai duba:

  • Idan mace tana da a kalla uku daga cikin alamomin cutar
  • Idan sinadarin da ke jikin makoko ya yi yawa a jikin mace
  • Akwai wasu gwaje-gwaje na musamman da likitocin kwakwalwa ke yi don gano cutar

Cutar tana da magani, kuma ana nasarar warkewa idan aka mayar da hankali wajen shan magani.

Bincike ya nuna cewa sau da yawa, samun tallafi daga 'yan uwa ko maigida ko makusantan mai fama da wannan cuta na taimakawa wajen samun waraka.

A al'umarmu ba a cika samun masu fitowa su bayyana cewa suna fama da wannan cuta ba, ko kuma suna jin alamunta.

Wannan ba ya rasa nasaba da tsangwama ko kyara da a kan nuna wa masu rashin lafiyar kwakwalwa, don haka ko mace ta ji alamun cutar tsananin damuwa bayan ta haihu ba ta iya gaya wa kowa bare ta je asibiti.

Wani lokaci kuma, mata ba su san cewa cuta ce suke fama da ita ba, sai su yi ta wahala su kadai.

Haka kuma, wasu matan na tsoron kada a ga sun gaza ko kuma sun haukace.

Rashin fahimtar cutar da abubuwan da ke haifar da ita kan haifar da rashin jituwa tsakanin mahaifiyar da maigidanta, ko mutanen gidan ko ma sauran 'ya'yanta idan tana da su kamar yadda Karima ta samu matsala da maigidanta.

Short presentational grey line

Yagana Gambo- Dauda ta ce matan da ke fama da wannan cuta kan ji tsanar jariransu amma a zahiri ba tsana ba ce.

"Sau da yawa, rashin sanin yadda za su yi da jaririn ne saboda za su ga abin sabo. Ga wasu kuma shayar da jariransu nono ne ke sanya masu damuwa a ransu," a cewarta.

Yagana ta ce matan da ke fama da wannan cutar kan ji gajiya a jikinsu, kuma wannan ma kan haifar masu da jin haushin jaririn a wani lokaci.

"Cutar kan sa wasu mata su ji alamominta sosai a lokacin da suke shayar da jaririnsu nono, don haka sai su ji takaici a lokacin kuma saboda jaririn ne a kusa da su sukan yi hushin ne da jariran," in ji Yagana.

Haka kuma, ta ce akwai matan da kan gamu da cutar idan haihuwa ta zo masu da tangarda, kamar ta Karima.

"A nazarin lafiyar kwakwalwa akwai abin da muke ce wa 'Post Traumatic Stress Disorder', kuma wannan kan jefa mata cikin kangin wannan cuta.

Short presentational grey line

Karima ta samu lafiya yanzu amma ta ce ba za ta taba mantawa da abin da ya faru da ita ba a baya.

"Ba zan taba mantawa da wannan lokaci ba saboda yanayi ne marar dadi. Amma dalilin cutar, na kara kusantuwa da Allah kuma na kara kaimi wajen addini," in ji Karima.

Duk da cewa wasu na alakanta cutar tsananin damuwa da rashin ibada ko rashin sanin addini, likitoci na cewa babu wata dangantaka tsakanin abubuwan biyu.

Sau da yawa a al'umarmu, a kan ce mutanen da ke fama da cutar tsananin damuwa na da aljanu ko kuma a ce mayu ne suka kama su.

Wani lokacin ma a kan yi tunanin sun haukace ne.

Amma Yagana Gambo- Dauda ta ce "Cutar tsananin damuwa cuta ce kamar ko wacce da kan kama dan Adam, babu abin da ya hada ta da rashin mayar da hankali kan addini ko maita."

Karima ta ce nan gaba idan ta tashi yin wata haihuwar, ba za ta sake amincewa a yi mata tiyata ba.

"Gara in haihu a gida da in je asibiti, saboda na dandana kudata. Likitocin sun gaya min a lokacin wai jaririyar ba ta kwanda yadda ya kamata ba a cikina amma daga baya na gano ashe akwai dabarun da za su iya yi su juya ta.

"Na fahimci kawai sun dai so su yi min tiyatar ne," in ji Karima.

A yanzu, tana gudanar da rayuwarta cikin farin ciki da kwanciyar hankali ita da mijinta da 'yarta.

Short presentational grey line

Karin labaran da za ku so ku karanta