Yadda wanda ya fara fafutukar a wanke hannu ya sha wahala

An yi wani lokaci a baya da daukar mara lafiya a kai shi asibiti ya zama abin kyama saboda abin da maras lafiya zai iya fuskanta.

Asibitoci a karni na 19 sun kasance wasu wuraren daukar cuta sannan ana amfani da tsaffin kayan aiki da ka iya salwantar da rayukan marasa lafiya.

A wancan zamanin, har gwara maras lafiya ya zauna a gida domin jinya maimakon zuwa asibiti kasancewar ana yawan mutuwa a asibiti fiye da a gida.

Kabari kusa

Asibitoci na zarnin fitsari da warin amai da sauran abubuwan kazanta. A lokacin ma'aikatan asibiti na yawo da kyalle domin rufe hanci saboda tsabar wari.

Likitoci ba su cika wanke hannuwansu ko kayan aiki ba. Hakan ne ya sa asibitoci suka yi kaurin suna da "kabari kusa".

Ana cikin wannan hali na rashin fahimtar cututtuka da asibitoci suka gaza yi, wani mutum dan asalin kasar Hungary mai suna Ignaz Semmelweis, ya yi kokarin yin amfani da kimiyya wajen dakile bazuwar cututtuka.

Ignaz Semmelweis ya yi kokarin aiwatar da tsarin wanke hannu a kasar Vienna a shekarun 1940s domin rage yawan mace-macen mata a dakunan haihuwa na asibitoci.

Tsarin wanke hannun ya kasance wani abu mai kyau amma kuma tsarin bai karbu ba sakamakon yadda abokan aikinsa suka rinka yi masa yankan bayaes.

To sai dai gaga baya dakta Ignaz Semmelweis ya yi suna "mai ceton iyaye mata".

A shekarar 1861, halayyar dakta Ignaz Semmelweis ta sauya ta zama wata iri inda bayan shekaru hudu aka kai shi gidan masu tabin hankali.

Wani abokin aikinsa ya dauke shi ya kai shi gidan masu tabin hankali na Vienna.

Amma bayan da Semmelweis ya fahimci abin da ake shirya masa ya yi yunkurin tserewa daga gidan, inda masu gadi suka yi masa dukan kawo wuka aka kuma kulle shi a wani bakin daki.

Bayan mako biyu ne kuma dakta Semmelweis ya mutu sakamakon wani ciwo da ya samu a hannunsa na dama. Ya mutu yana shekara 47.