Kun san likitan da ya taimaka wa CIA aka kama Osama?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, M Ilyas Khan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Islamabad
Wani likita dan kasar Pakistan wanda ya fallasa maboyar Osama Bin Laden zai daukaka kara don kalubalantar hukuncin da wata kotu ta yanke masa.
Wannan ne karon farko da aka yi sharia'ar Shakil Afridi a bainar jama'a. Alkalin ya dage sauraron karar zuwa 22 ga watan Oktoba bisa bukatar masu shigar da kara.
Rawar da Dakta Afridi ya taka a lamarin abin kunya ne babba ga Pakistan. Ya yi korafin cewa ba a ba shi damar kare kansa yadda ya kamata ba.
Ba a taba gabatar masa da tuhuma ba a hukumance game da rawar da ya taka wajen kashe mutumin da aka fi nema a duniya a shekarar 2011.
Tuhumar da Pakistan ta yi masa ta fusata Amurka har ma ta rage fan miliyan 27 na tallafin da ta saba ba ta - dala miliyan daya kenan kan kwace daya ta hukuncin a babbar kotun Peshawar.
Donald Trump ya yi alkawari ayayin yakin neman zabensa cewa zai fitar da Dakta Afridi "cikin minti biyu" idan aka zabe shi - abin da har yanzu bai faru ba.
Yayin da Amurkawa ke yi masa kallon wani gwarzo, a Pakistan kuwa mutane na kallonsa a matsayin maci amanar kasa.
Wata tawagar sojojin Amurka ta ruwa ta musamman ce ta kai samamen kashe Bin Laden tare da ficewa da gawarsa ba tare da martani ba.

Asalin hoton, Reuters
Hakan ya jawo wasu tambayoyi game da aikace-aikacen rundunar sojan Pakistan, wadda ke aikinta babu katsalandan, ko tana sane da zaman Bin Laden a cikin kasarta.
Har ya zuwa yanzu Pakistan ba ta bayar da hadin kai sosai ga yakin da Amurka ke yi da 'yan gwagwarmayar Musulunci.
Wane ne Shakil Afridi?
Dakta Afridi babban likta ne a yankin Khyber kuma saboda matsayinsa ya sa ya jagoranci gudanar da aikace-aikacen alluran rigakafin da Amurka ta samar a yankin.
A matsayinsa na ma'aikacin gwamnati, ya kirkiri shirin allurar rigakafin cutar shawara ta hepatitis B har a garin Abbottabad, inda a nan ne Osama Bin Laden yake boye.
Shirin da hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta yi shi ne ta shiga gida da Bin Laden yake domin karbar jinin daya daga cikin mazaunan gidan da zummar tantance kwayar halittarsa domin gano ko 'yan uwan Bin Laden ne.
Ana tunanin cewa daya daga cikin ma'aikatan Dakta Afridi ya shiga gidan kuma ya karbi jinin - sai dai babu tabbas ko wannan ne sirrin nasarar sojojin.
An kama Dakta Afridi ne ranar 23 ga watan mayun 2011 kwana 20 bayan kashe Bin Laden. Ana ganin yana dan shekara 40 da wani abu a lokacin.

Asalin hoton, Reuters
Ba a san wasu abiubuwa game da shi ba sama da cewa ya fito ne daga cikin iyali mai karamci sannan kuma ya kammala kwalejin aikin likita ta Khyber Medical College a 1990.
Iyalansa suna zama ne a boye tun bayan kama shi saboda tsoron hari daga 'yan gwagwarmaya.
Wane laifi aka kama shi da shi?
Bbayan an zargew shi cin amaanar kasa, an garkame shi a watan Mayun 2012 saboda samunsa da laifin tallafa wa kungiyar Lashkar-e-Islam wadda aka haramta.
An yanke masa hukuncin shekaraa 33 a gidan yari saboda zargin yana da alaka da kungiyar daga wata kotu kafin daga bisani aka rage zuwa shekara 23.
Kazalika, an zarge shi da taimaka wa mayakanta da aikinsa na liktanci da kuma ba su damar yin taruka a asibitin gwamnatin da yake shugabanta.
Iyalansa sun sha musanta zargin sannan lauyoyinsa ma sun ce kudin da ya taba biya shi ne na ruppe miliyan daya domin kubutar da kansa bayan an yi garkuwa da su a shekarar 2008.
Amma me ya sa ba a tuhume shi da taimaka wa Amurka ba?
Wannan abu ne da babu tabbas a kai, amma tabbas lamarin abin kunya ne ga Pakistan.
Duk da cewa ta fusata da cewa aikin Amurkar yin katsalandan ne ga 'yancinta, hukumomin tattara bayanan sirri sun ce ba su san da zamansa a kasarsu ba.

Asalin hoton, Reuters
Me yasa sai a kotu kawai ake jin labarin shari'ar tasa?
Zuwa yanzu dai sharia'rsa ta gudana ne a karkashin dokar Frontier Crimes Regulations tun ta lokacin Turawan Birtaniya wadda ake amfani da ita a yanki mai kwarya-kwaryar cin gashin kansa - kafin shekarar da ta gabata.
Su dai kotun al'adu shugabnnin al'umma ne suke jagorantarsu wadanda babu mai tilasta masu bin doka.











