Mutumin da nono ya fitowa zai karbi naira tiriliyan biyu

Risperdal tablets

Asalin hoton, Getty Images

An umarci kamfanin hada magunguna na Amurka Johnson & Johnson (J&J) ya biya diyyar dala bilyan $8 kimanin naira tiriliyan biyu ga wani mutum, bayan illar da maganin tabin hankali ya yi masa.

Maganin ya haddasa nonuwan Nicholas Murray sun kara girma kamar na mace a kirjinsa.

Wani alkali a jihar Philadelphia ta Amurka ne ya bayar da umarnin da a biya Nicholas Murray mai shekara 26 kudin, wanda shari'arsa daya ce daga cikin dubbai a jihar.

Lauyoyinsa sun ce wani kamfanin da ke hulda da J&J "ya fifita riba kan marasa lafiya" wajen hada kwayar Risperdal.

J&J zai daukaka karar, wadda alkali ya ce "kwata-kwata bai dace ba".

Farfesa Carl Tobias na jami'ar University of Richmond School of Law ya ce yana fatan za a rage yawan diyyar idan aka daukaka kara.

Kamfanin na kasar Amurka na fuskantar wata shari'ar game da wata hodar yara da ake zargin ya hada ta sinadarin asbestos.

Wadannan kari ne kan wata shari'ar kan yadda yake da hannu wajen samar da ganyen opioid mai kara kuzari a kasar Amurka.

A watan Agusta ma wani alkali a Oklahoma ya umarci J&J ya biya dala miliyan $572 bisa zargin ya taimaka wurin yin cinikin opioid "ta mummunar hanya".

Sai dai ya ce zai daukaka kara.

Risperdal tablets

Asalin hoton, Getty Images