Ko Trump ya fara dasawa da Erdogan kan Kurdawa?

Asalin hoton, AFP
Amurka ta ce za ta janye jiki domin bai wa Turkiyya damar far wa kungiyar mayakan Kurdawa da ke Syria wadanda kawayen Amurka ne a baya.
Mayakan kurdawa sun taka muhimiyyar rawa wajen yakar 'yan kungiyar IS, duk da cewa kasar Turkiyya ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda.
Amurka, wacce tana da daruruwan sojoji a gabashin Syria - ta fara janye dakarunta daga iyakar kasar inda Turkiyya ke son kafa sansaninta.
Mayakan Kurdawa na Syria sun bayyana wannan yunkurin na Amurka a matsayin cin dunduniya.
A watan Janairu, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar gurgunta tattalin arzikin Turkiyya muddin ta kai hari ga mayakan Kurdawa.
Sai dai wata sanarwa da fadar White House ta fitar ba ta ambaci mayakan Kurdawan ba.
Sanarwar ta biyo bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Trump na Amurka da kuma Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Asalin hoton, AFP
Me fadar White House ta ce?
''Turkiyya ta kusan fara shirinta da ta dade tana niyyar aiwatarwa a arewacin Syria,'' inji sanarwar.
''Rundunar sojin Amurka ta ce ba za ta yi katsalandan ba a aikin da sojojin Turkiyya za su yi ba, kuma Amurkar bayan ta fatattaki 'yan kungiyar ISIS daga yankin, za ta bar wurin gaba daya.''
Fadar White House din ta bayyana cewa Turkiyyar za ta dauki nauyin dukkanin mayakan IS din da mayakan Kurdawa suka kama shekaru biyu da suka wuce.

Asalin hoton, AFP
Sama da maza dubu 12 ne aka kama inda ake zargins u da alaka da kungiyar IS, kuma suna zaune ne a sansanonin mayakan Kurdawa da ke kudancin Turkiyya.
A kalla kusan dubu hudu a cikinsu 'yan kasashen ketare ne.
Wannan na nuni da wani sauyi a tsare-tsaren Amurka.
Wane martani Kurdawa suka mayar dangane da wannan sanarwa?
A ranar Litinin, mai magana da yawun mayakan Kurdawa na Syria wadanda ke zaune a yankin da mayakan IS suke a da sun yi watsi da yunkurin Amurka.
''Amurka ta dauki alkwarin cewa ba za ta bar sojojin Turkiyya su yi aiki a yankin ba'' inji Kino Gabriel a lokacin da ya shaida wa tashar larabci ta al-Hadath.
Ya kara da cewa '' Sanarwar da Amurkar ta fitar abin mamaki ne kuma za mu iya cewa hakan tamkar cin amana ne ga mayakan Kurdawa.''

Asalin hoton, EPA
Me Turkiyya ke shirin shiryawa?
A daren Lahadi, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa shi da Shugaba Trump sun yi magana ta wayar tarho kan sansanin da Turkiyyar za ta kafa a arewa maso gabashin Syria.
Ya bayyana cewa sansanin wanda ke da nisan kilomita 32 daga iyakar kasar za a yi amfani da shi wajen yakar 'yan tayar da kayar baya.

Asalin hoton, AFP/Getty Images











