An ceto mutum 500 a 'gidan kangararru' a Kaduna
Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraraon hirar Muhammad Annur Muhammad da DSP Yakubu Sabo Abubakar kan batun:
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun ceto kusan mutum 500 a wani gini da ake tsare da su a birnin Kaduna.
Baki dayan mutanen dai maza ne, manya da yara, wasu an daure su da mari ko sarka.
Wasu daga ciki ba 'yan Najeriya ba ne, amma sun ce an gana musu azaba, an ci zarafinsu, an kuma hana su zuwa ko'ina tsawon shekaru, kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo Abubakar ya shaida wa BBC.
Babu cikakken bayani a kan yadda suka samu kansu a wurin, ko da yake wasu sun ce kai su aka yi.
Sai dai ana kyautata zaton cewa ginin na makarantar allo ne.
'Yan sanda sun ce sun kai samame wurin ne, bayan an tsegunta musu cewa ba a gane take-taken mutanen da ke cikin ginin ba.

Asalin hoton, Kaduna Police Command

Asalin hoton, Kaduna Police Command

Asalin hoton, Kaduna Police Command

Asalin hoton, Kaduna Police Command
Kakakin yan sandan ya ce an kama mutum takwas da ake zargin suna da hannu a cikin lamarin.
DSP Yakubu Sabo Abubakar ya ce: "Bayan da muka samu bayanan sirri ne a game da makarantar sai muka kai wannan samame, muka kama shugaban da wasu daga cikin malaman makarantar.
"A yanzu kuma muna gudanar da bincike kafin daukar matakan gurfanar da duk wanda ke da hannu a gaban kotu."












