'Dalilin da ya sa aka kori shugabar ma'aikatan Najeriya'

Asalin hoton, Getty Images
A daren Laraba ne dai wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana nadin sabuwar shugabar ma'aikatan tarayyar kasar Dr Mrs Folashade Yemi-Esan.
Wanda hakan kai-tsaye ke alamta cewa an kori tsohuwar shugabar ma'aikatan wadda rikici ya dabaibaye, Mrs Wilfred Oyo-Ita.
Sanarwar ta ce 'An cire Oyo-Ita ne daga mukaminta domin a bayar da damar kammala binciken da hukumar bincike ta EFCC ke yi a kanta'.
Bayanin da ke cikin sanarwar ya nuna cewa an bukaci Oyo-Ita da ta fara wani hutun da ba ce ga ranar dawowarta ba.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawar Najeriya ta EFCC dai na binciken tsohuwar shugabar ma'akatan gwamnatin tarayya ce bisa zargin ta da hannu a badakalar wata kwantaragi ta kudi biliyan 3.
A baya dai hukumar ta EFCC ta kira tsohuwar shugabar, inda ta yi mata tambayoyi a kan al'amarin da ya jibanci kwantaragin.
Sabuwar shugabar ma'aikatan da aka nada Mrs Folashade Yemi-Esan kafin nadin nata ita ce babbar sakatariya a ma'aikatar man fetur ta Najeriya.
Sallamar Oyo-Ita dai na zuwa 'yan makonni bayan da hukumar EFCC ta fara bincike a kanta bisa zargin badakalar kwangila ta naira biliyan uku.
Ana kuma tuhumar tsohuwar shugaban ma'aikatan da wadaka da kudaden gwamnati ta hanyar yawan tafiye-tafiye domin samun alawus-alawus da safarar kudaden da ba na halas ba da kuma wawure kudaden gwamnati.
Yaki da cin hanci da rashawa?
Sharhi daga Ibrahim Isa
Tun gabanin a kawo wannan gabar hukumar EFCC ta sha yi wa Oyo-ita tambayoyi, bisa zargin da ya shafi rashawa, ciki har da batun yawan tafiye-tafiyen da ba gaira ba sabab, sai uwa uba zargin ba da wani kwantaragi ba bisa ka`id a ba da ya kai naira biliyan uku.
Kodayake, tsohuwar shugabar ma`aikatan ta sha musanta zargin.
Wannan dai bashi ne karon farko da manyan jami'ai a gwamnatin Shugaba Buhari ke tsintar kansu a tsakiyar rikicin da ya shafi rashawa har su kai ga rasa mukamansu ba.
Dama can dai zargin cin hanci da rashawa ne ya yi gaba da sakataren gwamnatin shugaban Buhari na farko a wannan mulkin nasa, wato Mista Babachir Lawal.
Wannan ya zo ne bayan wata badakala ta kwantaragin yanke ciyawa a tabkin Chadi da ake zargin yana da hannu a cikin wani kamfanin mai suna Rolavision, maganar da har yanzu tana gaban kuliya.
Irin wannan rikicin ne ya cinye tsohon babban Jojin Najeriya, mai shari'a Walter Onnoghen, wanda aka zarga da rashawa bayan an samu wusu miliyoyin naira da daloli a asussansa na banki.
Haka dai aka yi ta bugawa da shi, amma daga karshe ya tafi hutun dole, wanda daga can bai sake komawa kan mukaminsa ba.
A kwana-kwanan nan, an zargi Mr Obono Obla, wato shugaban wani kwamiti da fadar shugaban Najeriyar ta kafa don gudanar da bincike a kokarin kwato wasu kadarorin gwamnatin da hannu dumu-dumu a badakalar rashawa.
Shi ma, sai da aka fara da girke ofishinsa da wani bincike na sharar fage sannan gwamnati ta fito baro-baro ta ce sun raba-gari da shi, har aka bukaci hukumar yaki da rashawa ta ICPC da ta binciki al`amarinsa.
Wannan guguwar rashawa da ke bata garin tuwon manyan jami'ai a gwamnatin shugaba Buhari har suke rasa mukamansu dai ta sa masu sharhi a kan al'amura na kallon al'amarin ta fuskoki da dama.
Yayin da wasu ke cewa rashin sani ne ya sa gwamnatin ta yi tafiya da su tun da farko, wato dauko kara da kiyashi ko ta yi kisto da kwarkwata, wasu kuma na cewa himma ce kawai gwamnatin ta sa a aniyarta ta yaki da rashawa, wadda take ikirarin cewa ba sani ba sabo.











