Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun amince a kebe dabbobi a gandu — A.A. Sule
Gwamnatocin arewacin Najeriya sun yanke shawarar rungumar shirin gwamnatin tarayya na inganta harkar kiwo ta hanyar kebe dabbobi a gandu.
Sun yanke wannan shawarar ce sakamakon yakinin da suke da shi cewa sabon tsarin zai kyautata zamantakewa tsakanin makiyaya da manoma, tare da bunkasa tattalin arziki.
A baya dai tsarin ya sha suka daga wasu jihohi musamman na kudancin kasar, wadanda ke zargin cewa shiri ne na kwace musu sassan kasashensu don ba wa makiyaya.
Jihohi bakwai ne suka rungumi wannan tsari ciki har da jihar Filato, da Neja da kuma Nasarawa.
Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Abdullahi Sule, ya shaidawa BBC cewa makasudin daukar matakin shi ne tabbatar da zaman lafiya.
''Wannan mataki zai kawo zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma, zai sanya mutanen su zauna wuri guda a kuma samar da makarantu da asibitoci da samar da ruwan da za su shayar da dabbobinsu.
Ya kuma kara da cewa, "Za a kuma samar da zaman lafiya. Sannan akwai tsarin daukar ma'aikata tun daga malaman makaranta da likitoci a asibitoci''
Gwamnan na Nasarawa ya kara da cewa gwamnati ba ta kayyade girman filin da gwamnonin jihohin za su bada ba.
Ya ce hasalima kowacce jiha ta na da damar ba da filin da ta ke ganin za ta iya domin gudanar da aikin.
A baya dai gwamnatin Najeriya ta ce babu wata jihar da ta yi wa dole ta samar da Rugage domin killace dabbobin makiyaya kamar yadda wasu ke rade-radi.
Gwamnatin ta ce ba wai Fulani makiyaya ne kawai za su ci gajiyar rugar ba, duk wani mai sana'ar dabbobi zai amfana da ita kuma hanya ce ta magance rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci, ya ki cinyewa a Najeriya.
Haka kuma irin wannan rikicin na janyo asarar rayuka, da dukiya mai tarin yawa da raba mutane da muhallansu.