Hotunan 'yan Najeriyar da aka kwaso daga Afirka ta Kudu

Sawun farko na 'yan Najeriyar da suka tserewa hare-haren kin jinin baki daga Afirka Ta Kudu sun isa birnin Legas a ranar Laraba da daddare.

Mutum 188 cikin 600 na 'yan Najeriya da suka iso a sawun farko na 'yan ciranin da suka ce suna sha'awar dawowa gida, bayan hare-haremn kin jinin baki da aka kai a biranen Pretoria da Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Sun samu jinkiri na sa'o'i takwas kafin jirginsu ya bar babban filin jirgi na OR Tambo.

A cewar jakadar Najeriya na Afirka Ta Kudu, ba a taho da wasu mutanen ba saboda rashin isassun bayanai kan tahowa da yara da suke son yi.

Hargitsin ya jawo durkushewar dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu na nahiyar Afirka masu karfin tattalin arziki.

Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta ce jirgi na biyu zai tashi zuwa Johannesburg domin kwaso sauran mutane masu son dawowa, zuwa Najeriya.

Mutum 12 ne suka rasa rayukansu a hare-haren kin baki da aka kai wa mutane da kuma kasuwancinsu a Afirka Ta Kudu, ciki har da wasu baki guda biyu.

Duk da cewa Ma'aikatar Hulda da Kasashen Waje na Najeriya ta ce babu dan Najeriyar da ya mutu a harin, labaran bogi da aka yada a shafukan intanet sun tayar da hankulan jama'a.