Robert Mugabe: Hotunan rayuwar tsohon shugaban Zimbabwe

Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe lokacin da yake gaisawa da wanda yafi kowa kudi a nahiyar Afirka Aliko Dangote gabanin ganawar su a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Harare, ranar 31 ga watan Agustan 2015.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe lokacin da yake gaisawa da Aliko Dangote gabanin ganawarsu a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Harare, ranar 31 ga watan Agustan 2015.
Mugabe da Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo tare da tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a fadar gwamnatin Zimbabwe da ke Harare ranar 17 Nuwambar 2003. Sun tattauna a kan matsayin Zimbabwe gabanin taron kungiyar kasashe rainon Ingila da za a yi a Abuja a Disambar shekarar. Obasanjo ya ki ya fadi ko akwai yiwuwar za a gayyaci Mugabe taron na Commonwealth.
Bikin ranar juyin-juya hali karo na 32 a birnin Tripoli na kasar Libya ranar tara ga watan Janairun 2001. daga hannun dama tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe tare da takwaran sa na Libya marigayi Moammar Gadhafi da kuma tsohon shugaba Omar Hassan El Bachir na kasar Sudan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bikin ranar juyin-juya hali karo na 32 a birnin Turabulus na kasar Libya ranar 9 ga watan Janairun 2001. Daga hannun dama tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe tare da takwaransa na Libya marigayi Moammar Gadhafi da kuma tsohon shugaba Omar Hassan El Bachir na kasar Sudan.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga hagu lokacin da yake gaisawa da takwaran sa na Zimbabwe a wancan lokaci Robert Mugabe, daga dama kuma tsohon shugaban Tanzanian Jakaya Kikwete a taron shugabannin Afirka na musamman karo na 20, bayan da suka fito daga taron kungiyar Afirka ta AU ranar 27, ga watan Janairun 2013 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga hagu lokacin da yake gaisawa da Robert Mugabe. Daga dama tsohon shugaban Tanzania Jakaya Kikwete a taron shugabannin Afirka na musamman karo na 20, bayan da suka fito daga taron kungiyar Afirka ta AU ranar 27 ga watan Janairun 2013 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Tsohon shugaba Robert Mugabe lokacin da yake magana da tsohuwar ministar kudi ta Nigerian minister Ngozi Okonjo-lweala daga dama , Sarauniyar Buganda Sylvia Magginda Nnangareka daga tsakiya,a wani taron da aka yi a Harare babban birnin kasar Zimbabwe ranar 24, ga watan Mayun 2012.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaba Robert Mugabe lokacin da yake magana da tsohuwar ministar kudi ta Najeriya Ngozi Okonjo-lweala daga dama, Sarauniyar Uganda Sylvia Magginda Nnangareka daga tsakiya, a wani taron da aka yi a Harare babban birnin Zimbabwe ranar 24, ga watan Mayun 2012.
Robert Mugabe holds a press conference as newly elected prime minister of Zimbabwe, March 6th 1980 Robert Mugabe ya kira taron manema labarai a matsayin sabon Firaministan Zimbabwe a watan Maris na 1980.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An zabi shugaban jam'iyyar Zimbabwe African National Union (Zanu) Robert Mugabe a matsayin firaminista bayan da aka kawo karshen mulkin mallaka na tsirarun fararen fata a Rhodesia wato Zimbabwe a yanzu.
The Prince of Wales (left) with Robert Mugabe (second left), Prime Minister of the newly independent Zimbabwe (formerly Rhodesia), Joshua Nkomo and Foreign Secretary Lord Carrington during a dinner at Government House in Salisbury (now Harare)

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Mugabe ne kadai shugaban kasar Zimbabwe tun bayan samun 'yancin kai. Shi ne na biyu daga hagu a wannan hoton da aka dauka a watan Maris din 1980 tare da Yariman Wales da shugaban jam'iyyar Zanu ta Zimbabwe Joshua Nkoma da kuma Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Lord Carrington.
Margaret Thatcher and Robert Mugabe in 1980

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A wannan hoton, Mugabe ne da Firaministar Birtaniya Margaret Thatcher a shekarar 1980, yana neman wata hanyar sasantawa da Turawa tsoffin abokan gabarsa, inda ya ba su damar ci gaba da rikon baitil malin kasar.
Presentational white space
Ziyarar shugaban Zimbabwe Robert Mugabe kenan tare da mai dakin sa Grace a wata Majami'a da ke Hanoi, Vietnam a shekarar 2001

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu daga cikin al'ummar Zimbabwe na cewa al'amuran kasar sun fara tabarbarewa ne daga lokacin da ya auri sakatariyarsa Grace a shekarar 1996. Wannan hoton an dauke shi ne a shekarar 2001 lokacin da suka je wani yawon shakawa a Vietnam.
Presentational white space
Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton kenan lokacin da yake nuna wa Mista Mugabe wani abu a fadar gwamnatin kasar ta White House , a shekarar 1995.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A shekarar 1995 tsohon shugaba Robert Mugabe ya gana da takwaransa na Amurka Bill Clinton, sai dai a wancan lokacin tattalin arzikin kasar ta zimbabwe na ci gaba da tabarbarewa. Ya fuskanci matsaloli daga kasashen Yammaci, sai dai hakan bai hana shi fuskantar su ba.
Presentational white space
Robert Mugabe kenan lokacin da yake jawabi a wata Majami'a da ke Bulawayo, ranar uku ga watan Maris din shekarar 2008.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tsohon shugaban, wanda mabiyin darikar Katolika ne, ya ce Allah ya amsa masa addu'arsa ta samun galaba a kan makiyansa da kuma kwace filaye daga hannun fararen fata da ke neman mamaye kasarsa a wancan lokaci.
Wani dan kasar Zimbabwean kenan lokacin da yake nuna takardar sa ta kada kuri'a lokacin babban zaben kasar da aka gudanar ranar 27, ga watan Yunin shekarar 2008.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A yayin da tattalin arzikin kasar Zimbabwe ya yi mummunar tabarbarewa a shekarun 2000, an ci gaba da hasashen cewa Jam'iyya mai mulki ta tsohon shugaban a wancan lokaci ba ta da tabbas kamar yadda ake ganin ba za ta samar da wata mafita ba.
Robert Mugabe kenan, lokacin da yake sauka da ga kan mumbarin taron zauren Majalisar Dinkin Duniya, bayan ya gabatar da jawabi. ranar 22 ga watan Satumbar 2011, a birnin New York na kasar Amurka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tsohon shugaba Robert Mugabe ya ci gaba da fuskantar matsin lamaba daga kasashen Yamma. A shekara ta 2011, shafin kwarmata bayanai na Wikileaks ya ruwaito wata cibiyar difulomasiya ta Amurka na cewa Mista Mugaben na fama da cutar daji ta mafitsara. Hakan ya sanya aka yi ta hasashen mutuwarsa cikin kankanin lokaci.
Robert Mugabe kenan a wurin taron shugabannin Afirka karo na 22 a birnin Paris na kasar Faransa, ranar 21 ga watan Fabarairun 2003.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan ya jawo cece-kuce game da lafiyarsa. Mugabe ya fada a lokacin bikin ranar haihuwarsa na cika shekara 88: "Na mutu sau da dama a baya kuma na taso"
Robert Mugabe, 1976

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Robert Mugabe, 1924 - 2019
Presentational white space