Harin kunar bakin-wake a gidan biki ya kashe mutum 63

Lokacin karatu: Minti 1

An dai tayar da bam din ne a wani dakin taro da masu biki suka cika dankam a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, inda mutum 63 suka mutu sannan fiye da 180 suka jikkata.

Shaidu sun fayyace wa BBC cewa wata 'yar kunar bakin-wake ce dai ta tayar da bam din a tsakiyar masu shagalin bikin.

Da misalin karfe 10:40 na daren Asabar ne aka kai harin a yammacin birnin, inda mafi yawancin mutanen wurin musulmi ne mabiya mazhabar Shi'a.

Tuni dai kungiyar Taliban ta ce ba ta da hannu a harin. Har kawo yanzu kuma babu wata kungiya ko mutum da ya dauki alhakin kai harin.

Kungiyoyin masu ikrarin jihadi da ke bin mazhabar Sunna kamar Taliban da IS sun sha kai wa 'yan Shi'a hari a yankunan Afghanistan da Pakistan.

Shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani ya bayyana harin da aikin 'dabbanci' a shafinsa na Twitter.

Wani mai magana da yawun Taliban, Zabiullah Mujaheed ya ce kungiyar ta yi Allah-wadai da harin.

A wani sakon waya da ya aika wa 'yan jaridu, ya ce "Babu hujjar kai irin wadannan hare-hare da manufar kisan mata da kananan yara."