Me zai faru da Zakzaky bayan da ya koma Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da jagoran na 'yan Shia a Najeriya Ibrahim Zakzaky ya isa Abuja, hankali ya karkata ne kan makomarsa da kuma matakin da shi da lauyoyinsa za su dauka nan gaba. Abin tambayar shi ne, me zai faru da shi?

Tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin "bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa", sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan "mummunar halayyar da ya nuna".

Ta kara da cewa ya "saba ka'idojin kasa da kasa tare da yunkurin neman mafaka", lamarin da ya sa aka mayar da shi gida.

A farkon watan nan ne wata kotu a Kaduna ta bai wa malamin da mai dakinsa Zeenat, izinin tafiya Indiya domin duba lafiyarsu bayan shafe shekara kusan hudu a hannun jami'an tsaron Najeriya bisa zargin tayar da zaune-tsaye da yunkurin kisa.

Tun bayan kama shi a watan Disambar 2015, ake samun taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayansa a kasar, inda aka yi hasarar rayuka da kuma dukiyoyi da dama.

Me zai faru bayan ya koma Najeriya?

Da misalin karfe 12 na rana agogon Najeriya ne Zakzaky ya sauka a Abuja a jirgin Ethiopian Airlines. Kuma bayanai sun ce nan take jami'an tsaro suka yi awangaba da shi, ta yadda hatta 'yan jarida ma ba su samu sun ganshi ba.

Ya yi wannan tafiya ne dai tare da rakiyar jami'an tsaron Najeriya wadanda suka sa ido a kansa saboda ka da ya kaucewa sharuddan da kotu ta gindaya masa.

Dama dai Zakzaky da mai dakinsa suna rike ne a hannun gwamnati tun bayan kama su sakamakon tarzomar da ta kai ga kisan daruruwan magoya bayansa a watan Disambar shekarar 2015.

Da farko ana tsare ne da su a Abuja, kafin daga bisani a mayar da su Kaduna inda aka fara yi musu shari'a kan zargin tayar da hankali da kuma yunkurin kisa, zargin da suka musunta.

Kuma a karkashin wannan shari'a ne lauyoyin mutanen biyu suka nemi kotu ta basu damar fita kasar Indiya domin a duba lafiyarsu, suna masu cewa rayuwarsu "tana cikin hadari," bukatar da kotu ta amince da ita bisa wasu sharudda da suka hada da yi masa rakiyar jami'an tsaro.

Sai dai ganin yadda aka samu kiki-kaka a Indiyar, da kuma yanke shawarar mayar da shi Najeriya, za a iya cewa zai koma hannun gwamnati ne kai tsaye kamar yadda yake kafin ya tafi Indiya.

Mai magana da yawun kungiyar IMN ta mabiya Zakzaky, Ibrahim Musa, ya shaida wa BBC cewa malamin zai sake neman komawa wata kasar ne tun da dai kotu ta riga ta ba shi damar zuwa a duba lafiyarsa.

"Babu wani rudani domin kotu ta riga ta bashi dama. Kuma Malam ya ce kasashen Turkiyya da Malesiya da Indunisiya dukka sun ce za su iya yi masa wannan aiki," a cewar Ibrahim Musa.

Sai dai wasu na ganin batun sake fitarsa ba lallai ne ya zo da sauki kamar yadda magoya bayansa ke hasashe ba, ganin irin takaddamar da batun zuwansa Indiya ya haifar tun farko.

Ana hasashen cewa idan har zai sake komawa kasar waje, to sai kotu ta sake bayar da wani sabon umarni, domin wannan umarnin na tafiya Indiya ne kawai kuma ya je ya dawo.

Kuma alamu sun nuna cewa gwamnati za ta kalubalanci sake fitar da shi ganin yadda ta zarge shi da yunkurin "neman mafaka da saba ka'idojin kotu" a lokacin da ya je Indiyar.

'Dalilin barin Indiya'

Kusan dai za a iya cewa a yanzu murna ta koma ciki ga mabiyan Zakzaky wadanda suka yi marhabin da hukuncin kotun, wanda ake ganin zai taimaka wurin kawo karshen kika-kakar da ake yi tsakanin kungiyarsa ta IMN da kuma jami'an tsaro.

Lamarin da ya kai ga haramta kungiyar da kuma ayyukanta da wata kotun tarayya a Abuja ta yi.

Wannan bayani na dawowarsa gida Najeriya na kunshe ne a wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter.

Malamin ya bayyana cewa mahukuntan yankin da ya je neman magani a Indiya sun gaya masa cewa sun yanke hukuncin mayar da shi Najeriya.

Kuma za su kama hanyar dawowa nan da dan lokaci kadan.

Kawo yanzu babu bayani a hukumance daga mahukuntan Indiya ko kuma na Najeriya.

Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin kasar take rike da malamin addinin bayan wani rikici da mambobin kungiyarsa suka yi da sojoji a garin Zariya na jihar Kaduna.

Ko za a ci gaba da zanga-zanga?

Wasu na fargabar cewa mabiyansa za su ci gaba da zanga-zangar da suka saba yi tun bayan kama shi, wacce ta rinka kai su ga yin taho-mu-gama da jami'an tsaro.

Sai dai tun bayan haramta kungiyar da kotu ta yi, suka ce sun dakatar da wannan muzahara ko zanga-zanga da suke yi.

Kuma Ibrahim Musa ya ce za su mayar da hankali ne wurin sake shirin fitar da shi zuwa wata kasar domin duba lafiyarsa.

'Yan kasar da dama dai na fatan ganin an ci gaba da fafatawa tsakanin lauyoyin Zakzaky da na gwamnati a kotu, maimakon tashin hankali a kan tituna, wanda kan haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi - ciki har da na wadanda ba su ji, ba su gani ba.