Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnatin Najeriya ta fara 'magana da Boko Haram don ceto ma'aikatan agaji'
Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da Boko Haram kan wani yunkurin kubutar da Leah Sharibu da sauran wadanda kungiyar ke garkuwa da su.
Wannan ya biyo bayan wani bidiyo da ya bulla na wasu ma'aikatan agaji, inda wata mace daga ciki ta roki mahukuntan Najeriya da kasashen duniya da su taimaka wajen ganin an kubutar da su.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa yana fatan za a kubutar su ta hanyar tattaunawar da ake yi din.
Sai dai bai yi wani karin haske ba game da batun tattaunawar, kodayake ya bukaci masu garkuwar da su "tausaya."
Sannan ya ce wannan tattaunawar ba iya wadannan ta shafa ba, "har da Leah Sharibu" wadda tana daya daga cikin 'yan mata 'yan makaranta da Boko Haram ta sace daga garin Dapchi na jihar Yobe a watan Maris na 2018.
Sannan kuma bai fadi cewa ko Leah Sharibu tana raye ba, amma ya ce fadar shugaban kasa za ta dauki mataki, bayan tunanin da ake cewa an kashe dalibar.
Ma'aikatan agajin wadanda suke aiki da wata kungiyar bayar da agaji ta kasar Faransa mai suna Action Against Hunger, an sace su ne a jihar Borno.
Hakan ya faru ne lokacin da wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka yi wa ayarin motocinsu kwantan bauna, inda suka kashe direbansu.
Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa yana fatan za a kubutar su ta hanyar tattaunawar da ake yi din.
Kungiyar Action Against Hunger ta ce akwai alamun ma'aikatan suna cikin koshin lafiya, ta kuma bukaci da a sake su.
Wannan batun ya kara bayyana girman hadarin da ma'aikatan agaji suke fuskanta a lokacin da suke kokarin agazawa miliyoyin mutane da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin tafkin Chadi.
A bara ma an sace da kashe wasu ma'aikatan jinya mata biyu da ke aiki da kungiyar Red Cross a yankin arewa maso gabashin kasar.