Bai kamata a yi sulhu da 'yan bindiga ba - Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar ya ce an sha yin sasanci da 'yan fashi amma hakan bai kawo karshen kashe-kashe ba.

Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da kalubalen tsaro a arewacin Najeriya, musamman matsalolin hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.

Kuma sabuwar gwamnatin PDP ta Bello Mutawalle ta ce ta fara bin hanyoyin kawo karshen zubar da jinin da aka shafe shekaru ana kokarin magancewa, ta hanyar sulhu da wadanda take ganin sun jefa jihar halin da ta tsinci kanta a ciki.

Amma tsohon gwamnan jihar Abdul'aziz Yari wanda ake zargin al'amurran tsaro sun tabarbare a Zamfara a zamanin mulkinsa, ya ce ba za a taba sasantawa da 'yan bindiga ba, ba tare da nuna fin karfi ba.

"Sasanci, na yi na daya na yi na biyu kuma amma na uku na ce ba zan sake ba saboda hakan bai hana abin da ake a Zamfara ba na satar mutane da kasa-kashen mutane da dabbobin jama'a."

"Dole idan za ka yi sasanci sasanta sai an fito a fuskar fin karfi, cewa na fi ka karfi dole ka mika wuya," in ji Yari.

An dai sha amfani da karfi amma kullum ana kashe mutane a Zamfara.

Gwamna Mutawalle ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu ga shirinsa na sulhu, inda ya ce tun da farko ba a bi hanyoyin da suka dace ba.

Sabon Gwamnan wanda ake ganin yana daukar matakai ne irin wadanda aka dauka a baya, amma ya shaida wa BBC cewa matakan sun fara haifar da sakamakon da ake so.

Shirin sulhun ya shafi sasanta tsakanin mahara da 'yan-sa kai da jami'an tsaro da shugabannin Fulani.

Ya ce sakamakon matakin na sulhu yanzu an sako mutum 335 ba tare da masu garkuwa da su sun bukaci a biya wasu kudin fansa ba.

"Mun ja layi cewa duk mai laifi kowa ya ajiye makami ba tare da kuma ganin lafin wani ba.

Amma gwamna Yari ya ce ko a zamanin gwamnatinsa ya dauki matakai na yi wa 'yan bindiga afuwa, inda ya ce lokacinsa an kubutar da mutane, a sansancin da suka yi da Buharin Daji.

Tsohon gwamnan ya ce rikicin Zamfara ya shafi kowa da Hausawa da Fulani domin ba wata kungiya ba ce ke ayyukan ta'addincin.

Yari ya ce abin da suka lura shi ne akwai siyasa a cikin matsalar tsaron Zamfara, inda acewarsa "Akwai abubuwa da dama da aka kudundune na siyasa a ciki."

Ana ganin dai zamanin Yari ba a samu hadin kai ba tsakanin Sarakuna da gwamnati ba saboda shakkar salon tsarin mulkinsa.