Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin gaske ne an fara takardar yarjejeniyar aure a Kano?
Takardar yarjejeniyar da take ta yawo a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya musamman Whatsapp ta janyo cece-kuce a tsakanin al'umma, inda wasu ke ganin takardar tamkar yin wasa da aure ne.
Yarjejeniyar dai mai taken 'Takardar Yarjejeniya Kafin Aure' na dauke na alkawari tsakanin miji da mata, inda mijin ya sha alwashin yin duk wani abun kyautatawa ga maryar tasa kamar haka:
- Ciyarwa
- Tufatarwa
- Ilimantarwa
- Mutumtawa
- Kula da lafiya
Daga bangaren amarya kuma, ita ma akwai wurin da aka ware mata na sa hannu domin rantsuwa kan abubuwa kamar haka:
- Kyale ango ya kara aure
- Rashin cutar da shi ta hanyar amfani da makami ko guba
A karshen takardar ne kuma aka ware layuka guda tara domin sa hannun waliyan amarya da na ango da kuma alkali da da DPO na 'yan sanda na karamar hukuma.
Ga dai yadda aka tsara takardar:
Daga ina takardar ta fito?
Har kawo yanzu za a iya cewa ba a san daga inda wannan takarda ta fito ba kasancewar babu wani tambari da ke nuna wurin da ta fito.
Amma bazuwar ta a shafukan sada zumunta musamman Whatsapp da Facebook ya sa mutane sun fara tunanin ko gaskiya ne.
Watakila wasu mutanen kan iya tunanin cewa wannan takarda ta fito da kotunan da ke jihar Kano ne sakamakon yadda aka saba duk wata takardar yarjejeniya ko rantsuwa irin wannan na fitowa ne daga kotu.
Hakan ce ta sa BBC ta yi hobbasar bincikar gaskiyar lamari kan bazuwar takardar.
Tuni dai kotunan jihar ta Kano suka yi watsi da wannan takardar inda suka ce su ma ganin ta suka yi kamar kowa.
Mai magana da yawun kotunan jihar, Jibo Baba Ibrahim ya shaida wa BBC cewa takardar ta yi kama da ta labaran jabu ko kuma na kanzon kurege.
Me ya janyo yada takardar jabun?
Mai yiwuwa irin yadda mata kan yi amfani da makami ko kuma guba, a kan mazajensu a baya-bayan nan a Arewacin Najeriya ne ya janyo mutane suka fara yin raha.
An samu yanayin da mai gida ya yi zargin matarsa ta daba masa wuka, inda ita kuma matar ta yi zargin cewa yana yawan jibgarta ne.
Akwai irin wadannan shari'o'in masu yawan gaske dai a kotu, inda ma'auratan kan zargi juna da kokarin kisa.
Duk da cewa wannan takarda ba ta da sahihanci, amma alamu na nuni ga irin bukatar da jama'a ke da ita na samun wata hanyar da za ta kawo karshen badakalar da ke yawan faruwan tsakanin ma'aurata.
Menene labaran karya?
Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.
Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.
Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.
A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.
Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.
Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.
Hakan ne kuma ya sa ma'aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi'a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.
Yadda ake gane labaran karya
Akwai yiwuwar cigaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokacin da ake tunkarar zaban shugaban kasa a badi.
Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:
Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa. Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.
Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu. Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?
Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.
Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita. Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.
Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu ya ke.