Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tanko Yakasai: Ya kamata a kama Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya sha suka bisa wasikar da ya rubuta wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Wasikar, wacce Obasanjo ya aika ranar 15 ga watan Yulin 2019, ta kunshi sakonnin gargadi ga Shugaba Buhari musamman kan lamuran tsaro inda har ya ce Najeriya na daf da fadawa yaki idan Buhari bai sauya halinsa na ko in kula ba.
Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce matsalar tsaro a kasar na iya janyowa a kai wa Fulani harin ramuwar gayya, wanda ka iya jefa kasar cikin tashin hankalin kisan-kare-dangi irin wanda Rwanda ta fuskanta a baya.
To sai dai wasu jiga-jigai a siyasar kasar da tsoffin shugabanni sun yi wa Cif Obasanjo ca tun bayan da wasikar tasa ta bayyana.
Babban dan siyasa kuma daya daga cikin wadanda suka kafa Kungiyar Tuntuba ta Dattijan Arewa Tanko Yakasai ya yi Allah-wadai da kalaman Obasanjo inda ya ce sun nuna cewa ba shi da kishin kasa.
Ya ce "ban ga alamun kishin kasa a wasikun da Janar Obasanjo ke rubutawa ba. Asali ma, duka wasikun da yake rubutawa tsoffin shugaban kasa basu kunshi kalaman kishin kasa ba."
Tanko Yakasai ya ce wasikar da Obasanjo ya rubuta a lokacin mulkin Janar Sani Abacha ta jawo zarge-zargen cewa yana kokarin hambarar da gwamnati ne wanda kuma ya yi sanadiyyar daure shi.
Sai dai Tanko Yakasai ya ce lokaci ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari zai sake duba shawarwarin da aka tattara a taron kasa da aka yi a shekarar 2014.
Haka kuma, kungiyar Miyetti Allah ta Fulani ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya kama Olusegun Obasanjo bisa wasikar da ya rubuta masa.
Sakataren kungiyar, Saleh Alhassan ya bayyana wa BBC cewa ba makiyaya basu da hannu a matsalar rashin tsaron da ta addabi kasar don haka sun yi mamakin ganin tsohon shugaban yana danganta su da tada husuma.
A wasikar da ya rubuta, Obasanjo ya bukaci Shugaba Buhari ya dau matakin gaggawa kan karuwar satar mutane da kashe-kashen da a cewarsa Fulani Makiyaya ke aiwatarwa a kasar.
A shekaru biyun da suka gabata, daruruwan mutane sun mutu a rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da al'ummomi masu noma, musamman a yankin tsakiyar Najeriya.
A baya dai Obasanjo ya sha rubuta wasiku ga shugabanni kuma ya taba rubuta wa Shugaba Buhari ma daf da gudanar da zabukan 2019.
Ana iya cewa dai kisan Funke Olakunrin mai shekaru 58 ne ya tunzura Obasanjo ya rubuta wasikar.
Funke dai 'ya ce ga Reuben Fasoranti, wani mai fada a ji a kabilar Yarabawa.