Bayanan hoto, Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP sun ce su ne suka "lashe zaben na 2019 amma aka murde musu"
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta dage zaman shari'ar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar na kalubalantar zaben da ya gabata.
Dole ce ta sanya kotun daukar matakin sakamakon harin da aka kai wa shaidu daga bangaren jam'iyyar PDP akan hanyarsu ta zuwa Abuja daga jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa barayi ne suka afka wa mutanen akan hanyar ta su, inda dole suka bazama dazukan da ke kusa domin tsira da rayukansu.
Hukumar zabe ta INEC ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari na APC a matsayin wanda ya lashe zaben na watan Fabrairu, kuma tuni aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Sai dai Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP sun ce su ne suka "lashe zaben amma aka murde musu," a don haka suka garzaya kotun domin neman hakkinsu.
Tun da fari a ranar Juma'a, dan takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP sun gabatar da shaidu guda bakwai, da suka hada da jami'an kananan hukumomi, kamar yadda lauyan wanda ya shigar da kara Chris Uche ya bayyana.
Harwayau, jagoran lauyoyin PDP Levy Uzoukwu ya yi ikirarin shaidun da suka tsere sun tuntube shi ta wayar tarho.
Hakan ne ya sa ya yi kira ga kotun da ta dage zaman shari'ar domin su samu damar sake kiran shaidun su bayyana gabanta.
Alkalin da ke jagorantar shari'ar Muhammad Garba ya dage zaman kotun har sai ranar 15 ga watan Yulin nan da muke ciki.
Yadda sakamakon yake a kowacce jiha
Yaya zaben yake aiki?
Dan takarar da ya fi samun kuri'u ake ayyanawa a matsayin wanda ya yi nasara a zagayen farko, in dai har ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a kashi biyu cikin uku na jihohin kasar.
'Yan takarar shugaban kasa 73 ne suka yi rijista, amma an fi yin gwagwagwar ne tsakanin Buhari da Atiku.
Dukkansu sun fito ne daga arewacin kasar inda musulmai suka fi yawa, kuma dukkansu sun haura shekara 70, yayin da mafi yawan 'yan kasar da suka yi rijistar zabe 'yan kasa da shekara 35 ne.
Bayanan 'yan takarar shugaban kasa a 2019
Ga bayanan wasu 'yan takarar
Jam'iyya
Peoples Democratic Party (PDP)
Ranar haihuwa
25 ga watan Nuwamba 1946, Jada, Jihar Adamawa
Tarihi
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a 1999 - 2007
Ya nema kuma an ka da shi kujerar shugban kasa a 2007 a jam'iyyar AC
A 1998 an zabe shi gwamnan jihar Adamawa. Kafin a rantsar da shi ne PDP ta dauke shi a matsayin mataimakin shugaban kasa ga Olusegun Obasanjo inda suka ci zaben a 1999, an rantsar da Atiku a ranar 29 ga watan Mayu na 1999 a matsayin zababben mataimakin shugaban kasa.
Ya nemi kujerar gwamnan jihar Gongola ta da (wadda yanzu take (Adamawa da Taraba) a 1991, inda aka ka da shi.
Jami'in Kastam na tsawon shekara 25. 1964 - 1989
Jam'iyya
Alliance for New Nigeria (AN)
Ranar haihuwa
12 ga watan Mayu na 1971, Ibadan, Jihar Oyo
Tarihi
Kwararre a kan harkar kasuwanci da jawabi
Yana koyar da shugabannin kamfanoni da ke aiki a nahiyar Afirka da shugabanci a jami'ar Standford
Shi ne shugaban kamfanin Gemstone na gogar da mutane a kan shugabanci,
Jam'iyya
Young Progressive Party (YPP)
Ranar haihuwa
7 ga watan Mayu na 1963 a jihar Legas
Tarihi
Lawya kuma masanin tattalin arziki
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014, kuma mamba kwamitin kula da kudi
Moghalu tsohon jami'i ne a hukumar kula da harkokin wanzar da zaman lafiya na Maja;loisar Dinlkin Duniya dake a New York daga 1996 - 1997.
Tsohon jami'i mai ba da shawara kan harkokin shari'a na kotun majalisar dinkin duniya a kan Rwanda a 1997, daga baya aka yi masa karin girma zuwa jami'i mai hudda da jama'a na koyun.
Shi ne tsohon shugaban Global Partnerships and Resource Mobilization a hukumar kula da lafiya ta duniya
Jam'iyya
Jam'iyyar APC
Ranar haihuwa
17 ga watan Disamba 1942, Daura, Katsina
Tarihi
Shugaban kasa daga 2015 zuwa yanzu
Ciyaman din PTF, 1994
Tsohon shugaban kasa, 31 ga watan Disamba zuwa 27 ga watan 1985
Ya nemi kujerar shugaban kasa a 2003
Dan takarar jam'iyyar CPC a 2011 inda Jonathan na PDP ya ka da shi
Ministan Mai da Ma'adanai a 1976
Gwamnan Jihar Borno Fabrairu - Maris 1976
Gwamnan Arewa maso gabashin Najeriya a 1975 - 1976
Jam'iyya
African Democratic Congress (ADC)
Ranar haihuwa
24 ga watan Disamba na 1956 a Randa, Sanga, Jihar Kaduna.
Tarihi
Masanin tattalin arziki, Ma'aikacin banki, masani kan ci gaban kasa-da-kasa
Mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya a 2005 - 2007
Tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasa Jonathan a kan tattalin arziki da tsarin lamurra, mamba na kwamitin gudanar da tattalin arziki, kuma jami'i a bankin ci gaban Afirka.
Najeriya ce kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a Afirka, amma cin hanci da gazawa wajen zuba jarin abun da ake samu daga arzikin ya jawo matukar ci baya.
Kusan kashi daya bisa hudu na matasan kasar ba su da aikin yi.
Zaben cikin alkalumma
Masu katin zabe mutum miliyan 82, 344,107
Kashi 51 cikin 100 na masu kada kuri'a 'yan kasa da shekara 35