Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'yan bindiga suka rinka kabbara a kauyukan Katsina
Rahotanni daga Katsina na cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu satar mutane ne sun far wa wasu kauyuka guda uku a jihar inda suka shiga suna kabbara.
An dai ce maharan sun yi rera kalmar 'Allahu Akbar' wadda ke nufin Allah mai girma a lokacin da suka kauyukan.
Maharan dai sun shiga kauyukan Makera da Dan Sabau da Pawwa da ke yankin karamar hukumar Kankara.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Katsina, Gambo Isah ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, sun yi musayar wuta da maharan.
Bayanai sun ce 'yan bindigar wadanda suka shiga garuruwan a kan babura sun yi amfani da bindigogi da gurneti, inda suka kashe mutum shida, kamar yadda Isa Gambo ya shaida wa AFP.
Batun sata da garkuwa da jama'a dai na kara ta'azzara a yankunan jihar Katsina, inda a baya al'amarin ya fi shura a jihar Zamfara mai makobtaka.
Ko a baya-bayan nan sai da gwamnan jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari ya ce, za a yi karancin abinci a yankunan da ake samun matsalar tsaron.
Manoma dai da dama ba sa iya zuwa gona saboda fargabar abin da ka iya faruwa da su idan suka shiga daji.
Bayanai na nuna cewa yanzu masu sata da garkuwa da jama'ar sun karkata zuwa yankin karamar hukumar Kankara ne.
A baya-bayan nan kuma masu garkuwar sun mamaye yankin Matazu ne.
Sabon salon yin kabbara, Sharhi, Usman Minjibir
Abu ne sabo a ji masu sata ko garkuwa da jama'a a yankin arewa maso yammacin Najeriya suna rera kabbara a lokacin da suke far wa gari.
Za a iya cewa wannan ne karon farko da masu satar jama'a ke yin irin wadannan kabarbari a yayin hari a yankin.
An dai fi sanin irin wannan al'ada ta yin shelar 'Allahu Akbar' ga 'yan kungiyar Boko Haram da suka addabi yankin arewa maso gabashin kasar.
Da ma dai wasu masana harkar tsaro na cewa watakila kungiyar IS na amfani da 'yan bindigar.
Sai dai wasu na cewa 'yan bindigar na yin kabbarar ne domin su kawar da hankalin jama'a da ke yi musu kallon barayi.