An raba gurbataccen abinci a bikin matar shugaban kasa

Bayanan bidiyo, Yadda mahalarta bikin suka kama amai bayan ci shinkafa da kaji

An garzaya da mutane da dama zuwa asibiti bayan da suka halarci bikin murnar cika shekara 90 da haihuwar uwar gidan tsohon shugaban kasar Philippines Imelda Marcos.

Kimanin mutum 2,500 ne suka halarci fatin da aka shirya a birnin Manila, inda suka ci shinkafa da kaji.

Daga nan kuma aka fara garzayawa da wasu asibiti bayan da suka fara "yin amai", kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya ce.

Jami'an lafiya sun ce mutum 261 lamarin ya shafa. Amma rahotanni sun ce Mis Marcos ba ta cikinsu.

'Yar siyasar mai shekara 90 ita ce mai dakin tsohon shugaban mulkin kama-karya na kasar Ferdinand Marco.

Ta yi fice kan tsananin soyayyarta ga kayan kawa da kuma saitin takalmanta da suka haura guda 1,000.

Imelda Marcos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ta shirya gagarumin taro domin bikin zagayowar ranar haihuwartata a Manila
Dubban magoya bayanta ne suka halarci bukukuwan a wannan makon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban magoya bayanta ne suka halarci bukukuwan a wannan makon