Indiya: Rumfa ta fado kan masu bauta ta kashe mutum 14
A kalla mutum 14 ne suka mutu yayin da wasu 50 suka jikkata lokacin da ruwan sama da iska mai karfi suka jawo wata babbar rumfa ta fado a jihar Rajasthan ranar Lahadi.
Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wasu da dama sun mutu ne sakamakon jan su da wutar lantarki ta yi a yayin da rumfar ta kifa a kansu, wasu kuma sun mutu ne sakamakon fado musu da baraguzai ya yi.
Kusan mutum 300 ne suke wajen bautar a lokacin da abin ya faru, a cewar jaridar Hindustan Times.
Lamarin ya auku ne a gundumar Barmer da ke arewa maso yammacin jihar.

Asalin hoton, AFP
Minsitan agajin gaggawa na jihar Bhanwar Lal Meghwal, ya tuhumi masu shirya ibadar dalilin da ya sa ba su kashe wutar lantarki ba ganin yadda ake mamakon ruwan saman.
Tuni dai aka kaddamar da bincike kan lamarin.
Firaministan Indiya Narendra Modi ya ce lamarin abu ne mara dadi, a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Lahadi, inda ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X










