Al'ummar Malawi na zaben shugaban kasa

Masu kada kuri'a a Malawi suna rumfunan zabe domin zaben sabon shugaban kasa a zaben da aka kiyasta cewa shi ne mafi rashin tabbas da aka taba samu a kasar.

'Yan takarar dai bakwai ne ke fafata wa a zaben, amma uku ne ake ganin cewa za su iya samun nasara.

Shugaba Peter Mutharika zai tsaya takarar neman wa'adi na biyu, amma mataimakinsa Saulos Chilima da kuma Lazarus Chakwera ke kalubalantarsa.

A shekarar 1994, kasar da ke kudancin Afirka za ta koma zaben da jam'iyyu da dama ke shiga bayan da aka yi shekara 30 ana mulkin kama karya a kasar.

Dan takarar da ya yi nasara dai yana bukatar kashi fiye da hamsin na kuri'un da aka kada.

Mista Mutharika ne ya yi nasara a zaben 2014 da kashi 36.4 cikin 100.

Su waye manyan 'yan takarar?

  • Lazarus Chakwera - na jam'iyyar Malawi Congress Party
  • Saulos Chilima - na jam'iyyar UTM Party
  • Peter Mutharika - na jam'iyyar Democratic Progressive Party - shugaban kasar wanda ke neman wa'adi na biyu

Masu kada kuri'ar dai da suka kusan miliyan bakwai za su kuma zabi sabbin 'yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi.

Fiye da rabin wadanda za su kada kuri'a ba su kai shekara 34 ba kuma kuri'un matasa za su iya yin tasiri sosai.