Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda rayuwar 'yan jarida take a lokacin Boko Haram
Rikicin Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar ya shafi kusan kowane fanni na rayuwa kuma ya kawo kalubale ga yadda ma'aikata daban-daban suka tafiyar da ayukkansu.
'Yan jarida kamar sauran ma'aikata a yankuna da ake fama da rikicin na Boko Haram, irin ma'aikatan lafiya da na tsaro sun fuskanci jerin kalubale wanda ya sauya yadda suke gudanar da aiki.
Rikicin na Boko Haram dai ya fi kamari ne a jihohin Borno, da Yobe, da kuma Adamawa wadanda ke a yankin arewa-maso-gabashin Najeriya.
BBC ta tattauna da shugaban kafar yada labarun jihar Borno (BRTV), Adamu Isa Abadam, wanda ya ce sun kasance suna aiki a hali na dar-dar sa'ilin da rikicin Boko Haram ya yi kamari.
A cewarsa 'ta kai ga lokacin da sai dai ma'aikatanmu su kwana a wurin aiki, domin ba za ka iya zua gida ka kwana sannan ka dawo wurin aiki da safe ba'.
Ya kuma kara da cewa al'amura sun yi kamari, ta yadda 'yan jarida ba su isa su kira sunan Boko Haram a gidan rediyo ko na talabijin ba, kuma ko a wurin hira ma mutane ba su iya ambaton Boko Haram kai-tsaye.
Shi dai rikicin Boko Haram ya fara ne a shekarar 2009, lokacin da wasu matasa karkashin kungiyar suka kudiri aniyar yaki da gwamnatin Najeriya.
Sannu a hankali rikicin ya yadu zuwa kasashen jamhuriyar Nijar, da Chadi, da kuma Kamaru, masu makwaftaka, abinda ya sanya rikicin ya zamo wani abu da ya shafi kasashen da ke makwaftaka da tafkin Chadi baki daya.
A cikin hirar tasa da BBC, shugaban na kafar Radiyo da Talabijin na jihar Borno, ya ce 'akwai rasa rayuka da aka samu a tsakanin ma'aikatanmu da yawa'.
Ya kuma ce an rinka yi ma wasu 'yan jarida barazanar kisa matukar ba su ajiye aikinsu ba.
A yanzu haka dai an samu raguwa kan irin hare-haren da kungiyar ke kai wa a yankin na arewa-maso-gabashin Najeriya.
Sau da dama gwamnatin kasar ta sha yin ikirarin cewa ta ci galabar kungiyar, sai dai har yanzu akan samu hare-hare da akan alakanta da kungiyar jefi-jefi.