Abubuwa hudu da za su faru a wannan makon a duniya

Yau ranar Litinin ce, rana ta farko a wannan makon, don haka a yayin da muke yin kamar ba mu san dukkan abubuwan da za su faru a makon ba, to lallai ya kamata mu dan yi hasashen wasu abubuwan da za su faru cikin kwanaki bakwai din makon masu zuwa.

Ga dai wasu abubuwa masu muhimmanci da ake sa ran za su faru a duniya a wannan makon.

1) Za a bayyana sakamakon zabe mafi girma a duniya

Bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana kada kuri'a a babban zaben kasar Indiya, za a bayyana sakamakon karshe ne a ranar Laraba 23 ga watan Mayu.

Wannan ne zabe mafi girma da aka taba gani a fadin duniya - inda mutum miliyan 900 suka cancanci kada kuri'a - wato wannan adadin da ya dara yawan jama'an nahiyar Turai da kasar Australia.

Masu kada kuri'a za su zabi mutum 543 ne wadanda za su wakilce su a majalisar wakilan kasar.

Sai dai sakamakon farko yana nuna jam'iyyar Firai Minista Narendra Modi (BJP) ta kama hanyar samun nasara - kodayake wasu masu sharhi suna ganin hasashen ba lalle ne ya zama gaskiya ba.

2) Za a yi zaben kungiyar Tarayyar Turai

Daga ranar Laraba 23 zuwa Lahadi 26 ga watan Mayu, kasashen da ke kungiyar Tarayyar Turai za su kada kuri'arsu.

Kasashe mabobin kungiyar za su zabi wakilai fiye da 700 don wakiltar u a majalisar dokokin kungiyar.

3) Shugaba Buhari zai koma Najeriya

A ranar Talata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma gida bayan gudanar Umarah a kasar Saudiyya.

A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar a shafinta na Twitter a makon jiya, ta ce Sarki Salman Bin Abdulaziz ne ya gayyaci Buhari don gudanar da aikin ibadan.

"Ana sa ran zai koma gida Najeriya ranar Talata 21 ga watan Mayu," kamar yadda fadar shugaban ta bayyana.

4) Za a san zakarun Gasar Copa del Rey a Spain

A ranar Asabar ne za a san zakarun Gasar Copa del Rey na bana, bayan an buga wasan karshe tsakanin Barcelona da Valencia a filin wasa na Benito Villamarínm a kasar Spain.

Barcelona ce ta lashe Gasar La Liga ta bana, yayin da Valencia ta kare a matsayi na hudu.