'Zuwan Buhari Umarah daraja ce ga Najeriya'

Bayanan sautiHirar Garba Shehu kan tafiyar Buhari Saudiyya
Lokacin karatu: Minti 2

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren hirar da Mustapha Musa Kaita ya yi da Malam Malam Garba Shehu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umarah a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar a shafinta na Twitter ranar Laraba, ta ce Sarki Salman Bin Abdulaziz ne ya gayyaci Buhari don gudanar da aikin.

Sanarwar ta ce: "Shugaba Buhari ya amsa gayyatar da Sarki Salman Bin Abdulaziz ya yi masa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umarah.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

"Buhari zai bar Najeriya ranar Alhamis 16 ga watan Mayu, tare da masu taimaka masa na musamman.

"Ana sa ran zai koma gida Najeriya ranar Talata 21 ga watan Mayu."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

A wata tattauna wa da BBC ta yi da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ''a idon duniya gayyatar Shugaba Buhari ya je ya yi Umarah, daraja ce da kima aka baiwa kasar.''

Ya kuma yi karin haske dangane da ce-ce-ku-ce da wasu 'yan kasar da suke yi na yawan tafiye-tafiyen shugaban zuwa kasashen waje, inda ya ce ba za a rasa kyashi a zukatan masu irin wannan batutuwa ba, kuma ya bayyana cewa babu adalci a ce shugaban ba ya yawan zama kasar.

Shugaba Buhari ya ziyarci kasar ta Saudiyya a watan Fabrairun 2016, inda ya gana da mahukuntar kasar da kuma 'yan kasuwar kasar Qatar game da harkokin tattalin arziki.

Sannan kuma ya gudanar da aikin Umarar tare da gwamnonin Osun da Ogun da Zamfara da Borno da Katsina, da kuma Sarki Muhammadu Sanusi II da Oba na Legas.

Sai dai ziyarar ta wannan karon na zuwa ne mako biyu bayan mahukuntan kasar sun sako Zainab Aliyu wata daliba 'yar Najeriya da suka zarga da safarar miyagun kwayoyi bayan shafe wata hudu a tsare.

Musulmi da dama kan yi Umara cikin watan Ramadan saboda falalar da watan ke da ita.