An lalata tankunan dakon man fetur na Saudiyya a iyakar tekun Fasha

Image shows the dock for super tankers at the oil terminal of the emirate of Fujairah in the UAE - Wannan hoton na nuna karamar tashar jirgin ruwa inda ake rarraba man fetur a birnin Fujairah da ke Hadadiyar Daular Larabawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harin ya faru ne kusa da tashar jirgin ruwa ta birnin Fujairah da ke Hadadiyar Daular Larabawa

An kai hari kan tankunan dakon man fetur biyu na Saudiyya a kusa da kasar Hadadiyar Daular Larabawa a ranar Lahadi, a cewar ministan makamashi na Saudiyyar.

Lamarin, wanda ya faru kusa da tashar jirgin ruwa ta birnin Fujairah da ke kan iyakar Tekun Fasha a wajen mashigar teku ta ''Strait of Hormuz'' ya hallaka wasu daga cikin jiragen ruwan a cewar Khalid al-Falih.

UAE ta ce jiragen ruwa hudu ne aka kai wa harin, amma ba wanda ya rasa ransa.

Iran, wacce ta hada iyaka da mashigar, ta ce lamarin abin damuwa ne da kuma tausayi kuma ta yi kira da a gudanar da bincike.

Yankin da ke samar da a kalla kashi daya cikin biyar na man da ake samarwa duk duniya, na ci gaba da fama da rashin kwanciyar hankali.

Amurka dai ta aika jiragen yaki a cikin 'yan kwanakin nan domin tunkarar abin da ta kira alamun barazana daga Iran zuwa ga dakarunta da kuma sauran jami'an ruwa da ke aiki a yankin.

Iran dai ta yi watsi da dukkanin zarge-zargen a inda ta ce ba wata hujja.

A cikin watan da ya gabata, Iran ta yi gargadin rufe mashigar tekunta ''Strait of Hormuz'' idan an hana ta amfani da hanyar ta ruw,a bayan da Amurka ta yanke wani hukunci na cire tankunkumai kan manyan 'yan Iran masu sayen man fetur.

Me muka sani game da lamarin?

Har yanzu dai ba a bayyana bayanai sosai kan harin ba, wanda aka ce ya faru da karfe shida na safe, wato karfe biyun dare agogon GMT a ranar Lahadi, cikin tekun da ke yankin UAE kan iyakar Tekun Fasha ta kasar Oman, wato gabashin birnin Fujairah.

A yammacin ranar Lahadi ma'aikatar harkokin waje ta UAE ta ce wasu motoci hudu ne da ba a san daga inda suke ba, ake zargin cewa sun aikata lamarin, har yanzu dai ba a samu wanda ya rasa ransa ba ko kuma zubewar mai.

Ta kuma kara da cewa, ''Jami'an UAE sun dauki dukkanin matakan da ya kamata kuma suna gudanar da bincike kan lamarin.''

Ma'aikatar ta musanta dukkanin zarge-zargen a inda ta ce ba su da tushe, kuma ta jaddada cewa har yanzu harkoki na tafiya daidai a tashar.

Map of the Strait of Hormuz - Taswirar mashigar teku ta ''Strait of Hormuz''

A safiyar ranar Litinin, kamfanin dilancin labarai na Saudiyya ya ce Mr Falih ya fada cewa akwai wasu tankunan man fetur biyu na Saudiyya da aka kai wa hari su ma.

''Daya daga cikin jiragen na kan hanyarsa ta zuwa inda za a dora masa danyen man fetur na Saudiyya daga tashar jirgagen ruwa ta Ras Tanura, wanda zai kai wa abokan cinikin kamfanin Saudi Aramco da ke Amurka, a cewarsa.

Gidan talabijin na Saudiyya, Al Arabiya TV ya nuna abin da ya kira hotunan farko na jiragen da aka hallaka a ranar Litinin.

Ya kuma bayyan cewa sauran jiragen biyu da aka kai wa hari jiragen Norway ne da UAE.

Bayan wannan kuma, wani kamfani mai kula da jiragen ya ce wani abin da ba a san menene ba ya hallaka tankunan Norway a kusa da Fujairah.

''Masu aiki a jirgin dai ba su samu raunuka ba, duk da cewa jirgin ya huje,'' A cewar kamfanin Thome Ship management. ''Jirgin dai bai tattare da wata barazanar nutsewa.''

Wa za a dora wa alhakin?

Saudiyya da Hadadiyar Daular Larabawa ba su zargi kowace kasa ko kungiya ba.

Duk da haka dai, Mr Falih ya ce an kai harin ne domin takaita walwalar jiragen ruwa da kuma tsaron yadda ake rarraba kayayyakin man fetur zuwa ga mabukata duk duniya.

Ya kuma kara da cewa, kungiyoyin duniya suna na da alhakin tsare walwalar jiragen ruwa da kuma tsaron tankunan mai.