Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ganduje ya yi alkawarin rattaba wa dokar masarautu hannu
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin rattaba hannu ba tare da bata lokaci ba, ga kudurin nan da Majalisar Dokokin jihar ke shirin tura masa kan bukatar samar da wasu sababbin masarautu guda hudu daga masarautar Kano.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Abba Anwar ya aike wa manema labarai, ta ce Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba.
Ya ce sun samu labarin cewa wata kungiya wadda ya bayyana da masu kishin jihar Kano ce ta kai bukatarta ga majalisar jiha kan kara kirkiro wasu masarautu daga wadda ake da ita yanzu.
Gwamna Ganduje ya ce "A shirye nake da na rattaba hannu a wannan kuduri da zarar majalisa ta turo min ba tare da bata lokaci ba."
A ranar Litinin ne majalisar ta gabatar da wannan kudurin doka, kuma masarautun da ake son kirkirowa kuwa su ne Rano da Karaye da Bichi da Gaya.
Kuma majalisar ta sake zama na biyu kan dokar a ranar Laraba, inda rahotanni ke cewa kafatanin 'yan majalisar da suka halarta na goyon bayan kudurin dokar, yayin da 'yan majalisar na jam'iyyar PDP suka kauracewa zaman tun a ranar Talata.
'Yan majalisar sun kuma dage zaman nasu zuwa wani zama na sirri da za su yi nan gaba, wanda daga shi ne kuma za su yi zama na uku kan dokar da kuma mayar da ita doka.
Ci gaban Kano ko akasinsa?
Ganduje ya kuma ce "ai duk mutumin da ya zo da wannan irin bukata an tabbatar ya na da tsananin kishin jama'ar jihar Kano din ne. Da kuma jihar gaba dayanta.""Da zarar majalisa ta gama yin duk abubuwan da za ta yi a kan wannan kuduri, kuma suka kawo min, to ina mai tabbatar wa da al'umma cewar zan sa hannu kudurin ya zama doka nan take ba tare da bata wani lokaci ba," ya ce.Sannan kuma gwamnan ya tunasar da mutane cewa "dama ai tuntuni shekaru da yawan gaske da suka wuce an so a samar da wasu masarautun daga cikin masarautar jihar Kano, amma Allah bai yi ba."
A dalilin haka ya ce sai yanzu Allah Ya kawo lokacin da wannan abu zai tabbata.
"Ba za mu bata lokaci ba kuwa wajen tabbatuwar wannan aikin na ci gaba," acewarsa.Ya kara da cewa ya dau aniyar sa wa kudurin hannu ne ya zama doka, musamman ma saboda wannan wani abin alheri na wanda jama'ar Kano su ke maraba da shi.
Kuma hakan a cewarsa zai kara samar da ci gaba mai dorewa ga wannan jiha."Akwai tabbacin za a samu ci gaba na gaske a dukkanin bangarorin wannan jiha tamu mai albarka. Fatanmu ma shi ne kar abin ya ja wani lokaci," in ji Gandujen.
Sai dai wannan doka na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce musamman a jihar.
A hirarsa da BBC, Dokta Tijjani Mohammad Naniya na Jami'ar Bayero da ke Kano, kuma masanin tarihi, ya ce "ga duk wanda ya san tarihi tambayar da zai yi ita ce mai ya kawo wannan batu."
A cewarsa ana bijiro da batutuwa a wannan sabon tsari da ake ciki na dimokradiyya da ake gani ya kamata a bai wa kowa 'yancinsa.
Sai dai a cewarsa, kamata ya yi duk abin da zai taso ya kasance ya taso ne daga jama'a ba wai wasu kungiyoyi ba.
Dokta Naniya, ya ce "duk da cewa ana maganar 'yanci ai ita ma majalisa jama'a ne suka zabe ta, kuma ta san nauyinta shi ne ta kare mutunci da martaba da tarihi da al'adar mutane."
"Al'ada ce ke bambanta mutumin Kano da Katsina da yadda tsarin sarautar take, hakazalika ita ke bambanta mutumin Kano da na Borno, bambancin tsarin rayuwa da masarauta da kuma yadda tsarin zamantakewar jam'a take."
Karya karfin Sarki Sunusi?
Wannan dai wani yunkuri ne da ake dangantawa da kokarin rage karfin ko karya lakwan masarautar Kano.
Hakazalika, akwai wadanda suke ganin hakan ba ya rasa nasaba da rashin jituwa da ake ganin akwai tsakanin gwamnan jihar Kanon Abdullahi Ganduje da kuma Sarki Muhammadu Sunusi na Biyu.
Rahotanni sun ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya aike wa majalisar jihar kudirin bukatar amincewa da sake kirkirar wasu sabbin masarautu a jihar.
Wasu majiyoyin cikin gida kuma na cewa akwai zargin da ake cewa hakan baya rasa nasaba da bangarancin da ake zargin cewa sarkin na nuna wa a fanin siyasar jihar.
Sai dai Shugaban masu rinjaye na Majalisar Kanon Baffa Baba Danagundi, ya ce babu hannun bangaren zartarwa, bukata ce ta al'ummar wadannan yankunan.
Waiwaye
Kusan shekaru 40 da suka gabata an taba kirkirar sabbin masarautu a zamanin tsohon Gwamna Abubakar Rimi, lokacin da aka samu sabani tsakaninsa da marigayi Sarki Ado Bayero.
Sai dai daga baya a shekara ta 1983 Gwamnatin Sabo Bakinzuwo ta tarwatsa wadanan masarautu, inda aka hade dukkaninsu karkashin sarki guda.
An jima dai ana yada jita-jitar takun-saka da ake ganin akwai tsakanin Gwamnan mai ci da kuma Sarki Sunusi na Biyu, abin da ya kai ga a watanni baya aka ta yada cewa zai tube sarkin.