Bakin wani Aku ya ja masa kamun 'yan Sanda

Aku

Asalin hoton, Getty Images

'Yan sanda a Brazil sun tsare wani Aku inda suka zarge shi da yi wa masu siyar da miyagun kwayoyi sigina idan 'yan sandan suka karato inda suke.

Masu siyar da kwayoyin dai sun hori Akun ne ya rinka ihu yana fadin "mama, ga 'yan sanda" a yaren Portugal don ankarar da su idan 'yan sanda na shirin far masu.

'Yan sandan sun ce da zarar sun karato gidan da gungun masu siyar da kwayoyin suke, sai akun ya fara ihu.

Bayan kama Akun, 'yan sandan sun tsare shi a ofishinsu don yi masa tambayoyi kan abubuwan da ya sani game da masu siyar da kwayoyin.

Sai dai a cewar Alexander Clark, wani likitan dabbobi da rundunar 'yan sanda ta gayyato don yi wa Akun magana ya ce tsuntsun ya ki bayar da hadin kai don kuwa har yanzu bai ce komai ba.

Manema labarai sun tambayi 'yan sanda matakin da za su dauka a kan Akun, kuma sun ce za su mika shi ga hukumomin wani wurin ajiye dabbobi inda za a kwashe wata uku ana koya masa yadda zai rika tashi kafin a sake shi.