Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Sudan na bukatar mulkin farar hula cikin gaggawa'
Shugabannin da ke jagorantar zanga-zanga a Sudan sun bayyana wa mabiyansu cewa su ci gaba da zanga-zanga kan tituna har sai hakarsu da cimma ruwa.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Masu zanga-zangar a halin yanzu na bukatar bayar da mulki cikin gaggawa ga gwamnatin farar hula domin gudanar da mulkin dimokradiyya a kasar bayan hambarar da Shugaba Omar inda yanzu haka yana nan tsare.
Wannan kiraye-kirayen na masu zanga-zangar ya biyo bayan alamu da suka bayyana a zahiri na sojojin da suka yi juyin mulki a kasar na so su mulki kasar na shekaru biyu kafin gudanar da zabe.
Kungiyar Sudan Professionals Association wace ke jagorantar zanga-zanga a kasar ta wallafa a shafinta na Faceboook cewa ''muna kira ga sojoji da su tabbatar sun mika mulki ga gwamnatin riko ta farar hula cikin gaggawa.''
Ana fama da matsin tattalin arziki a kasar tun bayan da Sudan ta kudu ta balle daga kasar Sudan ta zama kasa mai zaman kanta a 2011 inda kuma Sudan ta kudu kasa ce mai arzikin man fetur.
Haka kuma, juyin mulkin ya biyo bayan watanni da aka shafe ana zanga-zanga kan tashin gwauron zabi na kayayyakin masarufi a kasar.
Me ya jawo wannan sabuwar takaddamar?
Bayan hambarar da gwamnatin Mista Bashir, an maye gurbin gwamnatinsa da gwamnatin soja inda ministan tsaron kasar Awad Ibn Auf ya ke jagoranta.
Amma masu gudanar da zanga-zanga a wajen shelkwatar rundunar sojojin kasar sun ki tafiya sakamakon kin amincewa da suka yi na Mista Auf a matsayin sabon shugaba saboda suna zarginsa a matsayin abokin tarayyar Mista Bashir.
A ranar Jumma'a, sabon shugaban ya bayyana cewa zai yi murabus ya ba Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ragamar jagorancin kasar wanda ana ganin Mista Abdelrahman babu cece-kuce a kansa sosai.
Amma duk da wannan yunkurin, hakan bai gamsar da masu zanga-zangar ba inda suke ci gaba da zama kan tituna a babban birnin kasar.
'Yan sanda a kasar sun bayyana cewa a kalla mutum 17 ne aka kashe tun daga ranar Alhamis.