Aure zai rika mutuwa cikin sauki a Ingila

Za a yi wa dokokin saki a Ingila da Wales garambawul ta yadda ma'aurata za su iya rabuwa da sauri, kuma cikin sauki.

A yadda dokokin suke a yanzu dole ne sai daya daga cikin ma'aurata ya zargi daya da zina ko wata dabi'a maras kyau kafin a ma fara maganar rabuwa.

Nan gaba idan aka yi wa dokar gyara, ma'auratan za su bayyana cewa suna son rabuwa ne saboda zamansu ba zai yuwu ba sam-sam.

Haka kuma idan dai har daya daga cikin mauratan na son rabuwa to dole ne a rabu, ko da dayan ba ya so.

Sakataren Shari'a na Birtaniya David Gauke ya ce sauyin zai kawo karshen suka ko dora laifin da maurata kan yi wajen gabatar dalilin neman kashe aure.

Wannan ya biyo bayan hukuncin kotun kolin kasar na kin amincewa da sakin da wata mata ta nema daga mijinta, bayan da mijin ya ki amincewa su rabu.

Tini Owens mai shekara 68 wadda ta fito daga yankin Worcestershire na son rabuwa da mijinta da suka yi shekara 40 tare saboda ta ce ba ta jin dadin zama da shi.

Amma kuma mijin mai suna Hugh ya ki yarda ya sake ta, kuma a kan haka kotun kolin ta yi watsi da bukatar matar ta neman saki.

Wanda hakan ke nufin za su ci gaba da zama a matsayin ma'aurata har zuwa shekara ta 2020.

Babbar mai shari'a ta Birtaniya, Baroness Hale, wadda tana daya daga cikin masu yin wannan shari'a ta dade tana neman a yi wa dokokin gyara, da cewa babu adalci a cikinsu.

Sabbin dokokin sun tanadi mafi karancin wa'adi na wata shida na rabuwa daga lokacin da aka shigar da karar neman kashe aure.

A karshen wannan wa'adi, za a bukaci wanda ke son a raba auren ya kara tabbatar da cewa lalle yana kan bakansa na neman a raba auren kafin a bayar da damar sakin.

Gwamnati ta ce wannan wa'adi zai ba wa mutum dama ya yi tunani a kan rabuwar, domin ko zai iya sauya shawara.

Haka kuma bayan wannan ma dukkanin ma'auratan wato mata da miji za su iya neman rabuwa gaba dayansu.

An dauki wannan mataki ne na sabunta dokokin bayan tuntubar jama'a da aka yi tsawon mako 12, wadda ta nuna jama'a sun amince da hakan sosai.

Mista Gauke ya ce yin garambawul a dokokin na shekara 50 zai iya hana rikici tsakanin iyaye, wanda yawanci ke bata rayuwar 'ya'yansu.

A bisa tanadin dokokin da ake da su yanzu, idan daya daga ma'aurata ya zargi daya da zina ko kuma wata dabi'a maras kyau a matsayin dalilin neman saki, to shari'ar za ta iya daukar daga wata uku zuwa shida, a tabbatar da rabuwar.

Amma kuma idan neman sakin ya kasance ba me wadannan dalilai ba ne, to rabuwar za ta iya daukar dogon lokaci.

To a nan sai ma'aurata sun gabatar da shedar da za ta tabbatar cewa ba sa rayuwa tare, wanda hakan zai hada da cewa suna zaune a gida daya, amma kuma ba sa kwana a gado daya, zuwa wani lokaci.

A Ingila da Wales za a iya fara shirya kashe aure ne bayan shekara biyu idan dukkanin ma'auratan biyu sun yarda a rabu, amma kuma shekara biyar idan daya bai yarda da rabuwar ba.

Amma a Scotland wa'adin zaman farawar shekara daya ne idan dukkanin ma'auratan sun yarda a kashe auren, idan kuma daya bai yarda ba shekara biyu ne.