Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum 50 sun mutu a hadarin mota a Ghana
Akalla mutum 50 ne suka mutum bayan wasu motocin bas biyu sun yi hadari a Ghana.
'Yan sanda sun ce motocin sun yi taho mu gama ne a garin Kintampo da ke tsakiyar Ghana da misalin karfe 2:00 na daren ranar Juma'a.
Babban jami'in 'yan sanda ACP Joseph Antwi Gyawu ya ce sun fara bincike kan al'amarin da ya jawo wannan mummunan hadarin.
Daya motar bas din tana da lamba GT 5694 18, sai guda mai lamba GT 3916 17 duka suna dauke ne da fasinjoji fiye da 50.
Har ila yau ya ce an garzaya da sauran wadanda suka ji rauni a wani asibiti da ke kusa.
Akwai wasu rahotanni da ke cewa daya daga cikin motocin ce ta kama da wuta, shi ya sa adadin mutanen da suka mutu ya yi yawa.