Me ya sa mutane ba su fito zaben kananan hukumomin Abuja ba?

- Marubuci, Umar Rayyan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Yayin da a sauran sassan Najeriya ake zabukan gwamnoni da 'yan majalisar jiha, a Abuja zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli ake yi a ranar Asabar.
Ana gudanar da zaben shugabanni da kananan hukumomi da na kansiloli a kananan hukumomi shida ne na birnin tarayyar.
Rahotanni sun ce ba a samu fitowar jama'a ba a unguwanni kamarsu Maitama da Asokoro da Garki da dai sauransu.
A lokacin da wakilinmu Haruna Tangaza ya kai ziyara fadar shugaban kasa da misalin karfe 12:00 na rana, ba a samu fitowar mutane ne ba a mazabar da ke fadar shugaban kasa.

Wani da ya je kada kuri'arsa a rumfar 022 a fadar shugaban kasa, Saidu Alhassan Haske ya shaida mana cewa: "mutane ba su fito zabe ba, idan aka kwatanta da zaben shugaban kasa."
"Wajen nan babu masaka tsinke, don wurin nan akwai mutane sun fi mutum 3,000 a wannan rumfar zaben lokacin zaben shugaban kasa," in ji shi.
Ya ce ana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Galibi ana ganin rashin kusanci tsakanin mazauna birnin wadanda yawancinsu ma'aikatan gwmnatin tarayya ne da kuma gwamnatocin kananan hukomomin na daya daga cikin dalilan da suka sa mutane ba su fita zaben ba sosai.
Akwai wasu da ke ganin rashin fitowar masu kada kuri'ar na da alaka neda cewa zaben na kananan hukumomi ne ba na gwamna ba.
Abuja ba ta da gwamna, sai minista wadda nada shi ake yi, ba zabensa ba, kuma yawanci mazauna garin sun fi sanin minista da ayyukansa fiye da na shugabannin kananan hukumomi.
Mai ya jawo raguwar masu kada kuri'a a zaben gwamnoni a jihohi?
Ko a sauran jihohin kasar ma inda ake zaben gwamnoni an samu raguwar masu kada kuri'a sosai ba kamar makon da aka yi zaben shugaban kasa ba.
Masu sharhi da dama sun bayyana rashin fitowar mutane da al'amura da dama.
Wata mai sharhi kan al'amura Rahma Abdulmajid ta ce Shugaba Buhari ya rikita mutane ta yadda ya fitar da sakonni iri biyu a lokuta daban-daban, "akwai lokacin da ya ce a zabi jam'iyyar APC sak a dukkan zabuka.
"Daga baya kuma aka sake ganin wani bidiyon inda yake cewa kowa ya zabi cancanta, wannan abu ya rikita da yawan masoyansa ta yadda suka rasa wanne za su kama. ta yiwu hakan ya hana da yawnsu fita zaben," in ji ta.
Hakazalika ta ce jama'a sun fi damuwa da zaben shugaban kasa kan na gwamnoni.
Kazalika Rahama tana ganin shigar malamai batun yi wa 'yan takara kamfe ma na iya zama dalilin rashin fitowar mutanen.
"Wasu Malamai sun yi ta wa'azi da nuna ga wanda ya dace a zaba. Hakan zai sa ko da akwai wadanda mabiyansu ke so kuma ya kasance suna girmam malaman, to za su iya yanke hukunci rashin kin halartar rumfunan zaben gaba daya," kamar yadda Rahama ta fada.












