Me ya sa sayen kuri'a ya zama ruwan dare a zaben gwamnoni?

Asalin hoton, Hukumar EFCC
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
A yayin da ake zaben gwamnoni a jihohi 29 na fadin Najeriya, wani al'amari da ke bai wa mutane da dama mamaki shi ne batun yadda ake sayen kuri'un mutane da kudi ko kayan masarufi ya zama ruwan dare gama duniya.
Wannan abu dai ya fara yawaita ne tun a ranar Juma'a wato jajiberin zaben. Sannan kuma wakilan BBC daga sassa daban-daban na Najeriya sun tabbatar da hakan, don kuwa su ganau ne ba jiyau ba.
Sayen kuri'un mutane dai a lokacin zabe babban laifi ne a dokar hukumomin kasar da ke yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.
A ranar Juma'a wakilan BBC da ke Jihohin Kwara da Legas sun ga yadda wasu jam'iyyu suke rabon kananzir da taliya da shinkafa ga mutane.
Haka zalika a ranar Asabar da ake gudanar da zaben, an ga yadda jam'iyyu ke rabawa mutane naira 200 ko 100 a wasu yankunan don su zabe su.
A ina ake rabon kudin?
Alal misali, a kusan daukacin jihohin kasar an samu rahotannin sayen kuri'un mutane.
Wata baiwar Allah da ta bukaci a sakaya sunanta daga Katsina, ta ce "Wallahi a kan idona na ga jam'iyyu biyu suna sayen kuri'un mutane. Daya jam'iyyar tana saya a kan naira 250 dayar kuma a kan naira 200.
"Ko ni sai da wakiliyar wata jam'iyya ta so latsa ni, amma ta ga ba fuska sai ta kyale ni," in ji ta.
A Legas ma an samu rahotannin sayen kuri'a da kudi ko wani abun amfani.

Haka zalika wakilin BBC da ke jihar Bayelsa ya ga yadda ake sayen kuri'u a kan naira 500, "ba ni gishiri in ba ka manda," wato ka dangwalawa jam'iyyar da suke so, su kuma su cake maka kudinka.
Wasu da dama sun shaida wa BBC cewa masu sayen kuri'un sun fi durfafar mata ne wajen yi musu tayin hakan, "Wallahi abun haushi sai ka ga an bai wa mace naira 100 kacal a sayi 'yancinta," kamar yadda wani ya shaida wa BBC.

EFCC ma ta yi kamu
Hukumar EFCC ma ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta kama wasu makudan kudade da take zargin za a yi sayen kuri'u ne da su a jihar Benue.
A kokarinta na kama wadanda ke dauke da kudin ne ma, wasu 'yan daba suka kai wa jami'an hukumar hari tare da lalata motar bas din da EFCC din ke sintiri da ita.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A ranar Juma'a da daddare ma, jami'an tsrao sun kama wata mota kirar Jif shake da kudi, wanda suka yi zargin cewa za a yi sayen kuri'u ne da su.
Kazalika wasu rahotanni sun ce EFCC ta kama babban akawun jihar Imo Uzoho Casmir, bisa zarginsa da taimakawa Gwamna Rochas Okorocha da halatta kudin haram har dala biliyan 1.05 a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki a ranar Asabar.
Hukumar dai tun a ranar Alhamis zuwa Juma'a ta tsaya kai da fata a filayen jiragen sama inda ake kai kayan zabe, don tabbatar da cewa babu makudan kudin da za a iya sayen kuri'u da su.

Asalin hoton, EFCC
Me doka ta ce kan sayen kuri'a?
Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati na EFCC da ta yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC sun bayyana sayen kuri'a a matsayin laifin cin hanci.
Ko a wani taron wayar da kai da ICPC ta gudanar a watan Disambar 2018 ta ce sayen kuri'a zamba ce a dimokradiyya.
A wancan lokacin shugaban hukumar ya shawarci 'yan Najeriya da su guji biyewa marasa kishin kasa masu yaudararsu da kudi ko abun masarufi.
"Idan har ku ka bar su suka yi nasara ta hanyar yin hakan, to kuwa za su tabbatar sun sace dukiyarku da aka ware don samar da ruwan sha da inganta harkar lafiya da ilimi da gina tituna idan har suka hau," a cewarsa.

Sharhi
Duk da cewa an yi sayen kuri'u lokacin zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya, amma ga dukkan alamu a wannan karon abun ya fi kamari.
Abun ya karu ne a wannan karon ganin cewa an yi a zaben bayan kuma wadanda suka yi sun sha, ba a kama su ba balle hukunci ya hau kansu.
Kuma wata illa da ke tattare da wajen rabon kudin shi ne da zarar masu rabon sun ga ana daukar hoto ko bidiyo don kafa shaida, to fa za su far wa mutum ne ko ma illata shi.
Malam Kabiru Sufi wani mai sharhi ne kan al'amuran siyasa a njaeriya kuma Malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, ya kuma shaida min cewa; "Kai ko kallo ka tsaya yi ba ma daukar hoto ba to yanzu sai ka ga an durfafo ka da niyyar far maka har a kai ga illata ka.

Asalin hoton, Sufi
To ko me ke jawo saye da sayar da kuri'un nan? Tambayar kenan da na yi wa Kabiru Sufi, ya kuma ce babban abun da ke jawo hakan shi ne talauci da ya yi yawa tsakanin mutane a kasar nan.
"An kai yanayin da ko mai rashin kaurin kudin da ka bai wa mutum zai iya sayar da 'yancin ya karba.
"Zan ba ki misali, jiya Juma'a a Kano, mun ga yadda mutane suka tare tun safe har dare a kofar gidajen manyan 'yan siyasa da ke sayen kuri'un don kawai samun dan abun da bai taka kara ya karaya ba.
"Kuma lokacin zabe ne kawai talakawa suke ganin suna da damar ganin 'yan siysasa daga nan kuma shi kenan," in ji Malam Sufi.
Ita ma wata mai rajin kare hakkin mata Rahama Abdulmajid ta ce an fi raina mata ne wajen nuna son sayen kuri'unsu "saboda ana ganin sun fi saukin saurin shawo kai."
Rahama ta ci gaba da cewa: "Mata ne talauci ya fi yi wa katutu, su ne yawanci ba su san abun da duniya take ciki ba saboda karancin ilimi da wayewa musamman a arewacin Najeriya, don haka su dai burinsu idan za su sami dan abun da za su biya bukatarsu ta gaggawa shi kenan.
"Sannan kuma suna ganin kamar lokacin siyasa ne kawai kakar samun wannan dama, don haka ido rufe za su sayar da abun da ya zam 'yancinsu," in ji ta.

Mece ce illar sayen kuri'ar talakawa?
Babbar illar da ke tattare da sayen kuri'un ita ce nakasta dimokradiyya. "Babu wata dimokradiyya da za ta samu ci gaban da ya dace idan dai har za a dinga amfani da halin tsanani da mutane ke ciki ana kara tauye hakkinsu ta hanyar sayen kuri'unsu don an san ba su da mafita sai yin hakan,' in ji Sufi.

Asalin hoton, EFCC
Illa ta biyu kuwa ita ce sayen kuri'u na iya sauya sakamakon zaben gaba daya. Malam Sufi ya ce a lokaci daya sai a sauya zukatan mutane da akidarsu wajen tursasa su su zabi wanda da farko ba shi suka yi niyya ba, don kawai an ba su kudi.
"Wani lokacin ma har hakan na sauya hasashen da tun farko aka yi cewa ga wanda alamu suka nuna zai ci, amma lokaci daya sai lamari ya sauya," a cewar Sufi.
Sannan wata babbar illar ita ce hakan zai sa ba za a dinga samun wakilci da shugabanci na gari ba, don kuwa duk masu fitar da kudi su sayi kuri'a to fa ana ganin lallai za su yi abun da duk za su iya don ganin sun ci riba a kudin da suka kashe ba ma mayar da uwar kudin ba kawai.
Ko ma dai mene be, lallai batun sayen kuri'u ba abu ne mai alfanu ga Najeriya da jama'arta ba, kuma ba abun da za ta yi sai nakasta kasar da kara durkusar da ita.












