Tasirin hotunan barkwanci na intanet a siyasar Najeriya

Daga Umar Jibrilu Gwandu, Malami a sashen Koyon Aikin Jarida

Bunkasar kimiyyar sadarwa ta intanet ta kawo wani sabon salon yakin neman zabe ga al'ummar Najeriya.

Halin da ake ciki, kari bisa ga yadda 'yan takara ke tallata manufofinsu a kafafen yada labarai, magoya bayansu ma sun tashi tsaye haikan wajen tallata ko kuma kushe 'yan takara a kafafen sadarwa na sada zumunta irinsu Facebook da WhatsApp da Instagram da dai sauransu.

Amfani da hotuna wajen yakin neman zabe ba wani sabon abu ba ne a siyasar duniya.

Amma na sauya hotunan asali zuwa hotunan barkwanci domin nishadantarwa da yada su ta kafofin sada zumunta wata al'ada ce da ta shahara a zabukan shugaban kasa da gwamnoni a Najeriya tun a shekara ta 2015.

Hotunan barkwanci da ake yadawa a intanet, wani sabon salo ne na sauya hotunan asali ta hanyar kara wa hotunan wasu siffofi, wani sashen jiki, wata halitta, jinsi ko kuma wani yanayi wanda da zarar mai kallo ya gani zai iya fahimtar an sauya hotunan daga yanayinsu na asali.

Damar ci gaba da sauyawa da kuma yada wadannan hotunan barkwanci da ke da ita ba tare da gano ko fayyaace makaginsu na asali ko mawallafinsu na farko ba; ta kara bai wa 'yan Najeriya damar amfani da kowane irin yanayin da lokaci wajen amfani da hotunan wajen yada manufofinsu ba tareda tsoron ko me hakan zai iya janyowa ba.

Manazarta hotunan bankwarci akan 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya da aka gudanar a shekara ta 2015, sun gano cewa an yi amfani da hotunan barkwanci akan 'yan takara a wancan zamanin wato Shugaban Kasa mai ci kuma dankarar Jam'iyyar PDP; Goodluck Ebele Jonathan da takwaransa na Jam'iyyar APC; Janar Muhammadu Buhari domin cimma manufofi da dama.

Manyan daga cikin jigon amfani da hotunan barkwanci wajen su na nuna cewa akwai kambamawa, kaskantarwa, fadakarwa, al'adantarwa da kuma nishadantarwa.

Bugu da kari an yi amfani da hotunan wajen kalubalantar 'yan takara, wayar da kan magoya baya, gugar zana, karkata alakar zance da kuma mayar da martini.

A zabukan shugaban kasa na bana ma an yi amfani da wadannan hotunan barkwanci domin isar da sakonni mabambanta.

Baya ga nishadantarwa, amfani da wadannan hotunan barkwanci na yanar gizo da 'yan kasar ke yi na kara tabbar da karbuwa, kimar da gudumuwar 'yan Najeriya ga tsarin mulkin dimokoradiyya.

Haka kuma, wadannan hotunan suna kara inganta huldar masu mu'amala da kafafen sada zumuntar zami.

Idan aka kara dubawa kuma za'a gano cewa ta hakan an sami bunkasuwar wayar da kan 'yan Najeriya akan siyasa da zabe, da kuma nuna masu wadanne 'yan kara suka fi samun karbuwa acikin al'umma.

Duk da kururuwar rashin 'yancin fadar albarkacin baki, kirkirawa da kuma yaduwar wadanan hotunan barkwanci suna tabbar da cewa 'yan Najeriya na cin gajiyar 'yancin fadar ra'ayinsu ba tareda samun nuna tsangwama ko kyama ba.

Yadda ake sauya hotunan su ba da wata ma'ana wadda daga farko babu ita, yana kara tabbatar da cewa 'yan Najeriya mutane ne masu basira da fasahar sarrafa mabambantan yanayi domin isar da sakonni masu nishadantarwa da kuma fadakar da juna.

Uwa-uba ma, a dai dai lokacin da a ke tuhumar wasu kafafen sadarwa wajen nuna bambamci da kuma bai wa wani bangare na 'yan siyasa dama fiye da daya, wadannan hotunan barkwanci sun ba da dama ta bai daya ga dukkanin 'yan Najeriya su yi musanyar ra'ayoyi a cikin nishadi.

Hakan ko shakka babu zai magance kullatar juna, bangar siyasa, kai ruwa rana da kuma fito-na-fito tsakanin magoya bayan 'yan takara.