Buhari ya yaba wa Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban kasar Olusegun Obasanjo murnar cikarsa shekara 82 a duniya.
Buhari ya bayyana Mista Obasanjo a matsayin "babban dan kishin kasa mai azama wanda ya cancanci yabo."
Ya ci gaba da cewa: "shugaban ya ba da gudunmuwa wajen wanzar da dimokradiyya da hadin kan Najeriya," kamar yadda ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar albarkacin ranar zagowar haihuwarsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo yana yawan sukar manufofin gwamnatin Buhari, inda ya rika rubuta wasiku da ke bayyana adawarsa a fili ga ci gaba da mulkinsa.
Mista Obasanjo ya mara wa dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, baya ne a zaben 2019.
Duk da akwai bambancin siyasa da ya shiga tsakanin mutanen biyu, Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce hakan bai hana su yaba masa ba kan yadda ya ba da gudunmuwa wajen ci gaban dimokradiyya a Najeriya.
- Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron hirar da muka yi da Malam Garba Shehu








