Prince Philip: Rayuwar mijin Sarauniya cikin hotuna

Duke of Edinburgh, 1977
Bayanan hoto, Duke na Edingburgh an haife shi a tsibirin Girka na Corfu ranar 10 ga Yunin 1921. Salsalar zuri'arsa ta tattaro zuri'ar iyalan gidan sarautar na Denmark, da Jamus da Russia da Birtaniya.
White Line 1 Pixel
Philip as a young boy

Asalin hoton, Getty Images / Alamy

Bayanan hoto, Yarima Philip shi ne da daya kwal ga Yarima Andrew na kasar Giris da Gimbiya Alice ta Battenberg.
Prince Philip of Greece, later Duke of Edinburgh, with his schoolmates at the MacJannet American school in St Cloud. The prince is the second boy from the left.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima ya fara karatunsa a kasar Faransa a makarantar Amurkawa ta Maclannet American School da ke St. Cloud, kuma ana iya gnainsa tare da abokan karatunsa.. Tun yana dan shekara bakwai ya koma ingila, inda ya zauna tare da danginsa zuri'ar Mountbatten da ke Ingila, inda ya rika halarta makarantar yamma ta Surrey.
Prince Philip at Gordonstoun aged 16

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Daga bisani ya halarci makarantar kwana ta Gordonstoun, wadda mashahuri masani a fagen ilimi Kurt Hahn ya kafa a Arewacin Scotland, inda ya shahara a harkar wasanni.
White Line 1 Pixel
Duke of Edinburgh, Royal Navy, Portsmouth

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A zamanin yakin Duniya na biyu, Yarima Philip ya kasance dalibi mai samun horon jan ragamar jirgin ruwan yaki, inda ya yi aiki a jirgin ruwan yaki na HMS Valian. Lokacin da aka tare jirgin ruwan yakin Italiya a kasar Girka cikin shekarar 1941, Philip ya bayar da umarnin baza hasken hange-hange, har ta kai ga ya hasko
White Line 1 Pixel
The engagement of Princess Elizabeth to Lieutenant Philip Mountbatten

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A hukumance aka sanar da baikonsa da Gaimbiya Elizabeth cikin watan Yulin 1947....
White Line 1 Pixel
Princess Elizabeth (latterly Queen Elizabeth II) and Prince Philip, the Duke of Edinburgh, pose for their official wedding photo at Buckingham Palace, 20 November 1947

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, ... sannan suka yi aure a ranar 20 ga Nuwambar wannan shekarar.
White Line 1 Pixel
The Duke of Edinburgh at the Roehampton Club, where he was playing for Cowdray Park in the semi-finals of the Roehampton Cup

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Ana iya ganin Yarima a nan yana wasan kwallon Polo a wajen shakatawa na Cowdray Park, inda ya kai ga wasan kusa da karshe na cikin kofin Roehamptom. Ya kasance daya daga jiga-jigan 'yan wasan Polo a kasar Birtaniya.
White Line 1 Pixel
The Duke of Edinburgh batting during the 12 a side cricket match between the Duke of Edinburgh and the Duke of Norfolk

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Basarake Duke ya kasance mai matukar son wasan kwallon Cricket. A nan kungiyarsa, ta hado da tsofaffin fitattun 'yan wasan Ingila, inda suka yi wa Kyaftin guda kawanya, wato Duke na Norfolk.
The Queen and Philip and their four children
Bayanan hoto, Duke da Sarauniya sun haifi 'ya'ya hudu, (daga hagu) akwai Edward da Andrew da Anne da Charles, a hoton da aka dauka cikin shekarun 1960.
Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh during a visit to a farm on their Balmoral estate, to celebrate their Silver Wedding anniversary

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Ana iya ganin ma'auratan lokacin da suka kai ziyara wata gona a katafaren gidansu na Balmoral, don murnar bikin cikarta shekara 25 da aure.
The Queen and the Duke of Edinburgh, both wearing Maori Kahu-Kiwi (Kiwi feather cloaks) at Rugby Park in Gisborne, on the North Island of New Zealand when they attended the opening of the Royal New Zealand Polynesian Festival as their Silver Jubilee Tour continues

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1977 Yarima ya yi wa Sarauniya rakiya lokacin da take bikinta na cika shekara 25 a karagar mulki. Ana iya ganinsu sanye da tufafin da aka saka da fatar Maori Kahu-Kiwi a wajen shakatawa na Rubgy da ke Gisborne, da ke Arewacin tsibirin kasar New Zealand, lokacin da suka halarci bikin sarautar New Zealand na Polynesian Festival a Fabrairu.
Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh wave as Concorde flies by the Royal Yacht Britannia as the royal couple neared Barbados

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Daga bisani cikin wannan shekarar dai ma'auratan 'yan sarauta sun rika daga wa jama'a hannu yayin da jirgin ruwan Concorde ya wuce a guje ta gaban jirgin ruwan sarautar Birtaniya na 'Royal Yacht Britannia.
The Union flag-draped coffin of Lord Mountbatten rests on a catafalque during the funeral service in Westminster Abbey. Royal mourners (l/r) Queen Elizabeth II, her husband The Duke of Edinburgh, Queen Elizabeth The Queen Mother and the Prince of Wales, 5 September 1979

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A Agustar 1979 an kashe dan uwan Sarauniya, Lord Louis Mountbatten a harin bom din 'yan tawayen Ireland na IRA da suka kai wa kwale-kwalensa a Ireland. Duke na Edingburgh ya komo Birtaniya bayan da ya samu labarin, bayan da ya kasance a jerin wadanda suka tuka jirgin da ya kai ga gaci a Normandy da ke Arewacin Faransa.
Duke of Edinburgh sitting atop an elephant while visiting the Kanha Game Reserve, 1983

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Kare halittu a muhallinsu al'amari ne na sha'awa da ya damfaru tsawon zamani a tattare da Duke na Edingburgh, don haka ya cancanci kasancewa Shugaban Asusun kula da Namun daji na duniya.
The Prince of Wales with the Princess of Wales, baby Prince Harry, Prince William, the Duke of Edinburgh, Prince Edward, Queen Elizabeth II and Princess Anne on the balcony of Buckingham Palace, London to watch the fly past

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1985 Duke na Edingburgh kewaye da iyalansa, wadanda suka hada da matashi Yarima Williams da Harry, a lokacin da suka taru don kallon shawagin jiragen sama a saman fadar Buckingham, inda rundunar sojojin Birtaniya da na kasashen rainon Birtaniya suka yi atisayen da ake yi wa lakabin 'Trooping the Colour.'
South African President Nelson Mandela, accompanied by the Duke of Edinburgh

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1996 Duke ya yi rakiya ga Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, lokacin da ya duba faretin sukuwar dawakai ta ban girma a ranar farko da ya kai ziyara kasar Birtaniya.
Queen Elizabeth II (right) and the Duke of Edinburgh (centre right) visit market stalls in Kingston town centre, during the Queen's Golden Jubilee visit to West London

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Yarima Philip ya tallafa wa Sarauniya (a ayyukanta) tsawon shekaru 60 da doriya na jan ragamar mulkinta, al'amarin da ya hada da bikin cikarta a karagar mulki shekara 50, wanda aka gudanar cikin shekarar 2002.
The Duke of Edinburgh attends the Presentation Receptions for The Duke of Edinburgh Gold Award holders, at the Palace of Holyroodhouse in Edinburgh, 2010

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Yarima sanya kyautar karramawa ta Duke na Edingburgh, wadda aka bullo da ita da manufar inganta rayuwar matasa, a shekarar 1956. A nan yana yin barkwanci da wadanda suka samu kyautar karramawa ta Duke na Edingburgh a Holyroodhouse cilkin shekarar 2010.
The Duke Edinburgh competes at the Sandringham Country show Horse Driving Trials held on the Norfolk Estate

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Duke ya ci gaba da shiga gasar wasanni har da tsufansa, al'amarin da ya hada da gasar tuka keken dawaki ta Sandringham cikin shekarar 2005.
Britain's Prince William kisses his wife Kate, Duchess of Cambridge, on the balcony of Buckingham Palace, after the wedding service, in London, 29 April 2011

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka yi dandazo a wajen fadar Buckingham don su gaishe da iyalan gidan sarauta bayan auren jikan Yarima Philip, Yarima William da aka yi da Catherine Middleton a shekarar 2011.
Prince Philip, Duke of Edinburgh, waves as he stand onboard the Spirit of Chartwell during the Thames Diamond Jubilee Pageant

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Watanni sha biyu daga bisani, Yarima ya kasance cikin koshin lafiya lokacin da ya raka Sarauniya taron tambarin sarauta a jirgin ruwan alfarma da kasaita, al'amarin da ya haifar da jikewarsu a ruwa lokacin bikin cikar Sarauniya shekara 60 a karagar mulki da ta gudanar a kogin pageant ranar 3 ga Yunin 2012. Shi da Sarauniya sun tsaya tsaye kyam har tsawon mintuna 80 ana tafiya, yayin da kananan jiragen ruwa dubu suka yi musu rakiya har tsawon mil bakwai daga Kogin Thames zuwa tulluwar gada. Sai dai Duke ya yi jinya a asibiti, inda ya yi fama da ciwon mara kafin bikin cika shekara 60 a karaga da aka gudanar ranar 4 ga Yuni.
Princess Anne attends equestrian eventing with Prince Phillip the Duke of Edinburgh,

Asalin hoton, Alex Livesey / Getty Images

Bayanan hoto, Bayan da ya murmure, ya samu cikakken koshin lafiyar da ya iya raka Gimbiya Anne ta kalli wasan tseren sukuwar dawaki na kasar Birtaniya, wadanda suka hada da jikarsa Zara Philips, wadda ta yi gasarta a yammacin gasar Olymfik din shekarar 2012.
White Line 1 Pixel
Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh as they attend a service at Westminster Abbey in central London to mark the 60th anniversary of the Queen's coronation

Asalin hoton, Jack Hill/The Times/PA

Bayanan hoto, A Yunin 2013 Duke ya halarci ibada a majami'ar Westminster Abbey don murnar zagayowar cikar Sarauniya shekara 60 da hawa gadon sarauta.
Signing the visitors book at Hillsborough Castle, Belfast

Asalin hoton, Brian Lawless / PA

Bayanan hoto, A shekarar 2014 ya yi wa Sarauniya rakiya a rangadin da ta kai Arewacin Ireland. An dauke shi a hoto yana sa hannu a littafin masu kawo ziyara gidan sarauta na Hillsborough Castle da ke Belfast.
Lighting beacon at Windsor Castle

Asalin hoton, Jonathan Brady /PA

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth II tare da rakiyar Duke na Edingburgh yayin da take kunna wutar farko kan tsirin kwarkwaro-kwarkwaro sama da 200 a wajen bikin cika shekara 70 da murnar samun nasarar yaki a Turai a gidan sarautar Windsor Castle.
The Duke of Edinburgh (left) and the Prince of Wales, during a visit to Poundbury, a new urban development on the edge of Dorchester, October 2016

Asalin hoton, Andrew Matthews / PA

Bayanan hoto, Basarake Duke da dansa Charles suna cikin annashuwa lokacin da suka kai ziyara Poundbury, wajen birni da ke gabar Dorchester, inda Sarauniya ta kaddamar da mutum-mutumin mahaifiyar Sarauniya.
Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh with an elephant at ZSL Whipsnade Zoo, where they officially opened the zoo's new Centre for Elephant Care as part of a visit to Bedfordshire

Asalin hoton, Chris Radburn / PA

Bayanan hoto, A Afrilun 2017 Basarake Duke ya raka matarsa wajen bude Cibiyar kula da giwa a gidan namun daji na ZSL Whipsnade da ke Bedfordshire. Si dai cikin Mayu ya bayar da sanarwar zai dakatar da gudanar da ayyuka a bainar jama'a tun da ya kai shekara 95, tare da cikakken tallafin Sarauniya.
Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh observing a minute's silence at the start of a garden party at Buckingham Palace in London, 23 May 2017

Asalin hoton, Dominic Lipinski / PA

Bayanan hoto, Sarauniya tare da Duke sun yi dshiru na minti guda a farkon bikin lambun fadar Buckingham da aka gudanar ranar 23 ga Mayun 2017 don tunawa da wadanda aka kashe (ko suka hallaka) a bikin dafdalar Ariana Grande da aka yi a Manchester.
The Duke of Edinburgh during a visit to the headquarters of the Royal Auxiliary Air Force's (RAuxAF) 603 Squadron in Edinburgh

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Basarake Duke ya kasance mijin Mai sarautar Birtaniya na tsawon zamani a tarihin Birtaniya.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.