An kashe mutum 66 a Kaduna a jajibirin zabe

Lokacin karatu: Minti 1

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe akalla mutane 66 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a ranar Juma'a.

Gwamnatin Kaduna da ta tabbatar da labarin ta ce harin ya fi shafar mata da yara kanana, inda aka kashe yara 22 da mata 12.

Harin kuma ya shafi rugagen Fulani da dama da ke cikin karamar hukumar Kajuru da suka hada da Ruga da Bahago da Ruga Daku da Ruga Ori da Ruga Haruna da Rugar Yukka Abubakar da Ruga Duni Kadiri da Ruga Shewuka da Ruga Shuaibu Yau.

Gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da harin duk da babu cikakken bayani game da dalilin kai harin.

Gwamnan jihar Nasir el-Rufa'i a cikin wata sanarwa da ya wallafa a Twitter ya bayyana cewa ya tura jami'an tsaro a yankin.

Kuma gwamnan ya ce tuni aka kama wasu daga cikin maharan, tare da yin umurni ga sarakuna da malaman addini a yankin su yi kira ga mutane a kauracewa kai harin fansa.

Ya ce hakkin jami'an tsaro ne su tabbatar da tsaro, kuma tuni aka kaddamar da bincike kan kisan.

An kai harin ne a jajibirin zabe, inda 'yan Najeriya ke shirin kada kuri'ar zaben shugaban kasa.