Babachir ya hallara a gaban kotu

Asalin hoton, THE GUARDIAN
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya a Najeriya Babachir David Lawal ya hallara a gaban wata kotu a safiyar Talata a Abuja babban birnin kasar.
A kwanakin baya ne dai hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a kasar wato EFCC ta ce ta kama tsohon sakataren.
Tuni dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kori Mr Lawal kuma ya kafa kwamiti domin gudunar da bincike kan zargin karkatar da kudaden da aka ware wa 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.
'Yan Najeriya sun ta bayyana korafe-korafensu musamman a kan tafiyar hawainiya da gwamnatin kasar take yi wajen shari'ar Mista Lawal.
Haka ma tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Buhari da rashin daukar mataki a kan mutane da ke da kusanci da shi, wadanda ake zarginsu da almundahana.

A watan Oktobar 2017 ne dai hukumar EFCC ta fara binciken tsohon sakataren gwamnatin Najeriya.
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC cewa hukumar ta fara bincikar tsohon sakataren gwamnatin kasar.
Hakazalika rahotanni sun ce hukumar ta hada wasu jami'ai masu bincike na musamman domin bincikar kwangilar yanke ciwaya ta naira miliyan 200 da aka alakanta ta da Babachir.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya dakatar Babachir da kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin Najeriya, Ayo Oke, daga bakin aiki ne a watan Afrilun 2017.
San nan ya kafa wani kwamitin bincike domin ya binciki zarge-zargen da aka yi musu na aikata ba daidai ba.
Shugaban dai ya bai wa kwamitin da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta wa'adin kwana 14 a matsayin lokacin da zai ba shi rahoton bincikensa.
Sai dai kwamitin bai samu ya mika mishi sakamakon binciken a kan lokaci ba domin shugaban ya tafi jinya kasar Birtaniya.
Da shugaban ya dawo daga Landan a watan Agustan 2017, bai dauki mataki akan rahoton kwamitin ba, lamarin da ya jayo wa gwamnatinsa suka.
Ranar 30 ga watan Oktoba ne shugaban ya kori Babachir Lawal da Ayo Oke daga aiki, matakin da masu suka suka ce bai wadatar ba.
Masu sukan sun bukaci gwamnatin ta gurfanar da mutanen a gaban kotu, inda wasunsu suka yi zargin cewa Shugaba Buhari ba ya so a hukunta makusantar shi idan suka yi laifi.
Sai dai mai taimaka wa Shugaba Buhari na musamman kan watsa labarai, Garba Shehu, ya musanta zargin yana mai cewa shugaban ba ya saka baki a aikin hukumomin kasar.











