Sojojin Najeriya biyar sun mutu a hatsarin jirgi

Jirgin soji
Bayanan hoto, A watan Fabrairun bara mayakan Boko Haram sun kai hari kan jirgin sojin Najeriya

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce jami'anta biyar ne suka mutu lokacin da wani jirginta mai saukar ungulu ya rikito kasa yayin yaki da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun sojin kasar, Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne lokacin da jirgin ke taimaka wa dakarun sojin kasa da ke yaki da 'yan Boko Haram a garin Damasak da ke jihar Borno ranar Laraba.

Sojojin da suka mutu su ne: Perowei Jacob, Kaltho Paul Kilyofas, Auwal Ibrahim, Adamu Nura da kuma Meshack Ishmael, in ji sanarwar.

Rundunar sojin ta ce an kai gawar sojojin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana musabbabin faduwar jirgin ba.

A baya-bayan nan sojojin Najeriya sun zafafa kai hare-hare maboyar 'yan Boko Haram, a yankin na arewa maso gabashin kasar.

Hakan na faruwa ne a didai lokacin da su ma 'yan Boko Haram, da mayakan da sukai mubaya'a ga myakan IS suke ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin.

Ana ci gaba da nuna fargaba kan yadda rashin tsaro ya sake kunno kai a jihar Borno da kewaye a daidai lokacin da Najeriya ke tunkarar babban zaben da ake sa ran za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.