Kawayen Amurka sun yi mamakin janye dakarunta daga Syria

Yawancin dakarun Amurka na girke ne a lardin Kurdawa da ke arewacin Syria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yawancin dakarun Amurka na girke ne a lardin Kurdawa da ke arewacin Syria

An soki matakin Shugaban Amurka Donald Trump na janye dukkan dakarun kasarsa daga Syria.

Mr Trump ya bayyana matakin ne ranar Laraba, yana mai ikirarin cewa an murkushe kungiyar IS.

Sai dai manyan kawayen Amurka, ciki har da sanatoci na jam'iyyar Republican da kasashen waje, sun ce ikirarin Mr Trump ba shi da kanshin gaskiya sannan suka ce hakan zai iya sa wa IS ta ake yin karfi.

US troops have helped rid much of Syria's north-east of the jihadist group, but pockets of fighters remain.

Sanatan jam'iyyar Republican Lindsey Graham, wada ke cikin manyan masu goyon bayan Mr Trump, ya bayyana daukar matakin a matsayin babban kuskure irin wanda tsohon shugaban kasar Barack Obama ya tafka.

Shi kuwa Sanata Marco Rubio cewa ya yi kalaman na Mr Trump kuskure ne da zai dade yana yi wa Amurka illa.

Ministan tsaron Burtaniya Tobias Ellwood ya caccaki ikirarin da Shugaba Trump ya yi cewa IS ba ta da wani tasiri, yana mai cewa barazanar da kungiyar ke da shi na da matukar yawa.