Shin wane ne marigayi Alex Badeh tsohon babban hafsan sojin Najeriya?

Asalin hoton, Nigerian Air Force
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kisan da aka yi wa tsohon babban hafsan sojan kasar Air Chief Marshal Alex Badeh mai ritaya a matsayin wani abin bakin ciki.
A cikin sanarwar da kakakinsa Femi Adeshina ya fitar, shugaban ya jajantawa iyalan janar din na soja da abokan aikinsa na soja da kuma gwamnatin jiharsa ta Adamawa.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta sanar da cewa wasu 'yan bindiga sun kashe tsohon babban hafsan dakarun tsaro na Najeriya, a yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga gonarsa da ke jihar Nasarawa.
Rundunar ta ce wasu 'yan bindiga ne suka harbe shi, lamarin da ya yi sandiyyar mutuwarsa.
Rundunar sojojin saman kasar ta wallafa wasu hotunan da ke nuna yadda 'yan bindigan suka halaka tsohon hafsan sojin.
Sanarwar da kakakin rundunar, Ibukunle Daramola ya fitar ranar Talata da daddare ta ce 'yan bindigar sun kai hari kan motar da Mista Badeh ke ciki lokacin da yake kan hanyar komawa gida daga gonarsa a kan titin Abuja-Keffi.
A cewar kakakin, tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu daga harbin bindigar da aka yi masa.
Tarihin rayuwar Alex Badeh

Asalin hoton, Facebook / Badeh
An haifi Alexander Sabundu Badeh a ranar 10 ga watan Janairun 1957 a garin Vimtim da ke karamar hukumar Mubi da ke jihar Adamawa.
Alex Badeh ya halarci makarantar firamare ta Vimtim da makarantar sakandare ta Villnova, inda ya sami kammala karatunsa na sakandare a shekarar 1976.
Daga nan ne ya samu shiga makarantar horas da sojoji ta NDA a 1977 cikin jerin dakarun da aka horas masu yin kwas na 21.
Ya kamamla karatunsa, inda ya zama Pilot Officer a ranar 3 ga watan Yulin 1979 kuma daga nan ya fara aiki tare da runduna ta 301 mai koyar da tukin jiragen sama ta sojojin sama na Najeriya.
Ya sami kwarewa a tukin jirgi kan samfurin jirgin sama mai suna Bulldog Trainer a 1979.
A tsakanin shekarun 1981 zuwa 1982, marigayi Alex Badeh ya halarci makarantar koyan tukin jiragen sama a Amurka da ke sansanin Vance Air Force Base.
Rayuwarsa a fagen aiki
Ya koma rundunar sojojin sama ta 301 inda ya rike mukaman babban matukin jiragen yaki da kuma na mai horaswa a kan jirgin yaki samfurin Bulldog da kuma na DO-228.
Marigayin ya rika samun karin girma a kan ayyukansa har ya kai ga zama Air Vice Marshall a 2008.
A shekarar 2012 ne aka nada shi hafsan sojojin sama na Najeriya, sannan a watan Janairun 2014 kuma aka nada shi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar.
Ya rike wannan mukamin har watan Yulin 2015, a lokacin da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi masa ritaya.

Tun bayan wannan lokacin, ya fuskanci tuhumar satar kudaden da aka ware domin sayen makamai a karkashin kulawarsa, wanda ya sanya hukumar EFCC ta kama shi kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.
An zargi Mr Badeh ne da wasu manyan jami'an soji da karkatar da kudaden da aka ware da niyyar sayen jiragen yaki, zargin da ya musanta.
Wasu rahotanni sun ce an ware kudaden ne a wani bangare na yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
A baya sojojin kasar da dama sun sha korafin cewa ba su da isassun kayan aikin da za su iya tunkarar mayakan kungiyar.
EFCC ta gurfanar da marigayin ne saboda ta ce ya sace dala miliyan 20 na kudaden makamai, kuma har wannan lokaci da aka kashe shi ba a kammala shari'ar ba.











