Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shekara 15 ina dauke da cutar HIV
Johnny Mathew, ya na dauke da cutar da ke karya garkuwar jiki ta HIV tsawon shekara 15.
Yayin da ake bikin tunawa da ranar cutar HIV ko Sida ta duniya, ya ce ya na amfani da wannan dama wajen karfafa wa masu dauke da wannan cuta guiwa, domin su rinka kula da lafiyarsu yadda ta dace.
Mathew ya ce 'Kai da ka ganin cewa kana dauke da cutar HIV, ka sani cewa za ka iya cika burinka na rayuwa, ku dube ni ku gani yadda nake cike da koshin lafiya ina walwala, idan na ce ma ku ina dauke da cutar da ke karya garkuwar jiki ba za ku yarda ba."
Ya kara da cewa "Mutane suna daukar cutar HIV kamar tikitin mutuwa ne, to amma ba ciwon ne ke kashe mutane ba, tsangwama ce daga iyali ke kashe mutane."
Ya kuma ja hankalin mutane cewa labarin da suke ji game da cutar Sida yawanci ba gaskiya ba ne.
Tun shekara ta 1988 ake ware ranar 1 ga watan Disamba a matsayin ranar ciwon Sida ta duniya. Rana ce wadda ake tuna wa al'umma cewa lallai ciwon Sida gaskiya ne, sannan kuma abu mafi muhimmanci shi ne a tunatar da al'umma cewa domin mutum na dauke da cutar ba shi ne ke nufin karshen rayuwarsa ba.
A wannan rana hukumar lafiya ta duniya tana kara wayar da kan al'umma kan cutar HIV da yadda za su kare kansu ko kuma kula da kansu idan suna dauke da ita.