Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi zanga-zangar adawa da ziyarar Yariman Saudiyya a Tunusiya
Daruruwan 'yan Tunusiya suna zanga-zangar adawa da ziyarar da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ke yi a kasar, a yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce ka kisan fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi.
Masu fafutuka da kuma 'yan jarida sun yi maci a tsakiyar babban birnin kasar tunis, suna ihun cewa Yarima mai jiran gadon Saudiyya mai kisan kai ne kuma ba a maraba da shi a Tunisiya.
Wasu majiyoyi na Tunusiya sun ce an kafe wani katon hoton Yariman a ofishin kungiyar 'yan jaridar kasar da ke nuna shi dauke da zarto - wanda ke nufin da shi aka sassara Mista Khashoggi.
Yarima Muhammad wanda ya sha yin watsi da zargin hannu a kisan, yana ziyarar ne a kasashen Larabawa, irin ta ta farko da yake yi tun bayan kisan Mista Khashoggi.