Buhari da Atiku sun raba kawunan 'yan Kannywood

Da alama zaben da za a yi a Najeriya a 2019 zai fi wadanda suka gabace shi ta fuskar rabuwar kawunan 'yan Kannywood da ke mara wa mabambantan 'yan takara baya.

Bayanai sun nuna cewa ba a taba samun adadin jaruman Kannywood da suka fito fili suka nuna alkiblarsu kamar a wannan lokaci ba.

Hasalima, tuni manyan jarumai irinsu Ali Nuhu da Adam A. Zango da Fati Washa suka ziyarci fadar shugaban kasa da ke Abuja inda suka bayyana shirinsu na mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya a yunkurin da yake yi na sake lashe zaben 2019.

Kazalika, jarumai irinsu Sani Danja, Fati Muhammad da Maryam Booth da Mika'ilu Bn Hassan Gidigo suka sha alwashin ganin tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ke takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP, ya kai batensa a zaben 2019.