Ana binciken halittun da matukiyar jirgi ta gani a sama

Cockpit

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matukan jirgin sun ga wasu halittu tashi da tsananin haske a sararin samaniya

Hukumar kula da harkokin jiragen sama ta kasar Ireland na binciken rahoton bullar wasu fitulu masu hasken gaske da kuma wasu halittu a yankin kudu maso yammacin kasar.

Abin ya faru ne da misalin karfe 06:47 na ranar Juma'a 9 ga watan Nuwamba a lokacin da wata matukiyar jirgin sama na kasar Birtaniya ta tuntubi sashen da ke lura da sauka da tashin jirage na Shannon.

Tana son ta sani cewar ko sojoji na gudanar da atisaye a wurin saboda akwai wani abu da ke matukar tafiya da sauri.

Sai dai mai kula da saukar jirage ya sanar da ita cewar babu wani atisaye da ake yi.

Matukiyar jirgin saman da ya taso daga birnin Montreal na kasar Canada zuwa filin jirgin saman Heathrow na London ta bayyana cewar akwai wani "haske mai tsanani" da kuma wasu abubuwa da suka tunkari bangaren hagu na jirgin kafin su juya suka nufi arewa".

Ta yi mamakin ko menene amma ba wai taho mu-gama ya tasamma yi da jirgin ba.

Haka shi ma wani matukin jirgin sama na Virgin ya bayar da shawarar cewa zai iya kasancewa tauraruwa mai wutsiya ko kuma wani abu da ke kokarin fadowa duniya.

Twitter

Asalin hoton, Twitter

Ya ce akwai karin wasu "halittu biyu da ke biye da tauraruwar mai wutsiya" wandanda ke da matukar haske.

Matukin jirgin ya kara da cewar ya fara ganin wani haske guda biyu wadanda suka tsallake jirgin a guje.

Daya matukin jirgin kuma ya bayyana cewar yanayin saurin tafiyar da tauraruwar ke yi ya yi kama da na sararin samaniya, wanda ya nunka saurin sauti sau biyu.

grey line

Wacce irin hallita ce?

Apostolos Christou, wani masani kan sararin samaniya daga cibiyar kula da duniyoyi da ke sama ta Armagh, ya bayyana cewar abin da matukan jirgin suka gani ba komai ba ne illa wani nau'in kura da ke kokarin fadowa cikin iskar duniya cikin yanayi hanzari mai yawa.

"Shi ne abin da ake kira da tauraruwa mai wutsiya" a cewar sa.

"Bisa dukkan alamu halittar na da matukar haske, akwai kuma yakinin cewar wani bangare ne daga jikin hallitar mai girma.

"Ba zan iya cewa komai ba daga bayanan matukin jirgin ba, amma zai iya kai wa girman goro ko kuma tufa."

Shooting star

Asalin hoton, Getty Images

Masanin ilimin taurarin samaniya ya ce watan Nuwamba wata ne da ake yawan samun kai kawo a cikinsa na irin wadannan hallittu.

"Kazalika akwai wani dan sassa da ke rabuwa da haliitar sannan kuma suka tashi suka tsallake jirgin saman, abin da ya kamata a ce a san zai faru idan ya kasance babban dutse ne daga sararin sama idan zai sauka a kan iskar duniya, zai iya kasancewa kuma ya rabu da sashinsa.

grey line

"Sakamakon rahotanni daga matuka jirgi kalilan a ranar Juma'a 9 ga watan Nuwamba, na bayyanar wasu irin halitu a sararin samaniya hukumar IAA ta aike da wani rahoto.

"Za a binciki wannan rahoton ne ta hanayar da aka saba yin bincike na boye bayyanar yadda abu ya kasance".

Mai magana da yawun filin girgin sama na Shannon ya ce ba dai-dai ba ne hukumar filin jirgin saman su yi magana a kan bincike da IAA suke gudanarwa.