Me ya sa Najeriya ke amfani da tsofaffin jirage?

Wani bincike da sashen kula da lafiyar jirage na Palnes Spotters ya gudanar ya ce jiragen saman Najeriya sun kasance a sahun gaba ta fuskar tsufa a nahiyar Afirka.

Binciken ya ce daya daga cikin jiragen saman kasar ya shafe shekara 28 yana aiki, idan aka kwatanta da sauran takwarorinsu a Afirka.

Sai dai kwararru sun ce lafiyar jirgin sama ba a yawan shekarunsa yake ba, illa dai yana bukatar kula da lafiyarsa bilhakki.

A Afirka an yi nuni da cewa daya daga cikin jiragen Najeriya shi ne mafi tsufa da ya kai shekara 28 yana aiki - wani abu da suka ce ya sha bamban idan aka kwatanta da wasu jiragen kasashen nahiyar kamar Kenya da Ruwanda da Habasha da sauransu da ba su wuce shekara biyar zuwa 14 suna zirga-zirga ba.

Sai dai sashen kulawa da bincike a kan harkokin jirage na Planespotters.net ya ce wani daga jirgin Najeriya yana cikin wa'adin shekara 11 yana aiki.

Captain Ado Sanusi kwararre a kan harkokin jiragen sama kuma manajan daraktan kamfanin Aero Contractors, ya ce tabbas akwai tsoffafin jirage da ake amfani da su a Najeriya.

Amma ya kara da cewa "idan ana kula da su yadda ya dace tsufan nasu ba zai zama wata matsala ba sosai."

Wasu masana harkokin jiragen sama a Najeriya dai na cewa jirgin sama ba ya tsufa illa dai ya na bukatar tsawon wani lokaci a sake masa na'urori da injina wanda kan dawo cikin hayyacinsu kamar sabo.

A shekarun baya dai an sha samun hadururrukan jiragen sama a Najeriya wanda wasu daga 'yan kasar suke zargin watakila saboda tsufa da kuma rashin kulawa ce.

To amma hukumomi a kasar sun ce lafiyar jirgi ba a tsufa take ba, face dai yana bukatar gyara da kulawa akan kari kamar dai yanda dan adam ko mota ke neman ba su kulawa.

A Najeriya dai hukumomin kula da harkokin lafiyar jiragen sama sun tashi haikan domin tabbatar da kowanne jirgi ya samu cikakken koshin lafiya kafin shigowa da kuma lokacin daukar fasinjoji, wani lamari da aka shaida na tsawon shekaru.

Matsanantan matakan da hukumomi a kasar kan dauka dai sun taimaka wajen samun koshin lafiya da rage matsalolin jiragen sama idan aka kwatanta da shekarun baya da kan zo da salwantar rayuka da dinbin dukiya.