Me Rabi'u Kwankwaso ya je yi Kano?

Asalin hoton, Kwankwaso RM/Facebook
Tsohon gwamnan Kano kuma mai wakiltar mazabar Kano Tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yana gudanar da wata ziyara ta kwanaki irinta ta farko a jihar tun da ya bar kujerar gwamnan Kano.
Sanata Kwankwaso ya ziyarci birnin na Kano ne ba tare da sanar da cewa zai kai ziyarar ba, abin da ya zo wa magoya bayansa da dama ba zata.
Wasu dai musaman 'yan Kwankwasiyya na cewa ziyarar ta Kwankwaso ta firgita gwamnatin Kano, ta Abdullahi Umar Ganduje.
To sai dai kwamishina watsa labaran jihar ta Kano Malam Muhammad Garba ya ce sam ziyarar ba ta dadasu da kasa ba.
Muhammad Garba ya ce duk wanda ya dubi ziyarar zai tabbatar da cewa ba ta yi armashi ba.
A cikin kwanakin, tsohon gwamnan ya ziyarci wasu wurare a birnin Kano domin yin ta'aziyya da kuma sada zumunci.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shaidawa BBC cewa lokaci ya yi da ya kamata a ce ya je Kano, kasancewar shekara uku ke nan rabonsa da jihar.
Abubuwan da Kwankwaso ya yi a Kano
1. Gaisawa da masoyansa da abokan arziki

Asalin hoton, Kwankwaso RM/Faccebook
Babban abin da ziyarar ta sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a Kano ita ce ganawa da masoyansa da abokan arziki, musamman wadanda ba su taba ganinsa ba tun bayan barinsa mulkin Kano.
Duk da cewa ba a shelanta cewa sanatan zai kai ziyara Kano ba, kuma ba yakin neman zabe ya je ba, mutane da dama sun yi dafifi a hanyoyin da dan siyasar ya bi, domin su gana da shi.
Haka kuma mutanensa da dama sun ringa kai masa ziyara a gidansa domin su gana da shi, kasancewar wannan ne karon farko da wasusunsu suka samu irin wannan damar.
2. Ta'aziyya
Sanata Kwankwaso ya ce ya kuma yi amfani da lokacin ziyarar a Kano domin yin ta'aziyyar wasu da rashe-rashe da aka yi a Kano, wanda bai samu damar zuwa ta'aziyya ba.
Daga cikin wadanda Sanata Kwankwaso ya tsara zuwa yi wa ta'azaiyya akwai iyalan Shaikh Isyaku Rabi'u, da na Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule, da na Magajin Garin Kano, Alhaji Inuwa Wada, da Sarkin Fadar Kano, Alhaji Suke Gaya, da AVM Mukhtar Muhammad da kuma iyalan Shaikh Mudi Salga.
To sai dai dan siyasar ya ce gidan Malam Isyaku Rabi'u kadai ya iya zuwa saboda yadda masoyansa suka yi dafifi a kan hanyoyi.
3. Ya zauna da 'yan takara

Asalin hoton, Kwankwaso RM/Facebook
Daya daga cikin muhimman abubuwan da Kwankwason ya yi a yayin ziyarar ta sa jihar da ya yi wa gwamna sau biyu, ita ce, ganawa da 'yan takara na jam'iyyar PDP.
Sanatan ya kuma gana da wasu 'yan PDP din da suka yi takara amma ba su samu nasara a zabukan fitar da gwani ba
4. Ziyarar Sarkin Kano

Asalin hoton, Kwankwaso RM/Facebook
A yayin ziyar da Kwankwaso ya kai Kano, ya kai wa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ziyara a fadarsa.
Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa ya ziyarci sarkin ne domin girmama shi a matsayinsa na uba ga al'ummar Kano.
Ziyarar ta Kwankwaso Kano dai na zuwa ne bayan an kammala zabukan fitar da gwani, kuma ake shirin fara yakin neman zabe gadan-gadan.
A baya Kwankwaso ya shirya zuwa Kano, to sai dai hukumomin tsaro sun ba shi shawarar cewa ka da ya je, saboda tsoron za a iya samun rikici tsakanin magoya bayansa da na gwamnan jihar mai ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Su dai magoya bayan Kwankwason sun yi watsi da hanzarin na jami'an tsaro, inda suka yi zargin cewa gwamnatin jihar ce ta hada baki da 'yan sanda domin a hana shi zuwa.
To sai dai 'gwamnatin da 'yan sanda sun musanta zargin na tsohon gwamnan Kano.
Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnan jihar mai ci Abdullahi Umar Ganduje, da kuma wanda ya gada Sanata Kwankwaso, jim kadan bayan barin Kwankwaso kujerar gwamnan jihar.
Sanatan ya ce zai ci gaba da zuwa Kano, amma ba zai je Kano ya tare ba.











