Sojojin Najeriya sun kwato wasu kauyuka 8 a Borno

Makaman Boko Haram

Asalin hoton, @HQNigerianArmy

Bayanan hoto, Sojojin sun yi wa mayakan Boko Haram ne kwantan-bauna
Lokacin karatu: Minti 1

Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin kwato wasu kauyuka da dama daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Sanarwar da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce samamen da rundunar hadin guiwa ta 25 a Chibok da ta 28 a Damboa suka kaddamar a Gumsari da Gambori a jihar Borno sun yi nasarar kakkabe 'yan Boko Haram a kauyuka kamar Litawa da Kashmiri da Dole da Mulimari da Mudachira da Njaba da Bale da Gambori

Sanarwar ta ce rundunonin sun kaddamar da farmakin ne a cikin dare a ranar Juma'a.

A cewar sanarwar, sun yi wa 'yan Boko Haram shigar ba-zata, inda mayakan suka gudu.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Sai dai sanarwar ba ta fadi ko akwai wasu daga cikin mayakan da aka kashe ba a gumurzun, amma ta bayyana cewa mayakan sun gudu sun bar kayayyakinsu da suka hada da keke 17 da wayoyin salula da jarkar fetir da abinci da kayan kwanciya da sauransu.

Sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da wannan ikirarin na sojojin na Najeriya.

Duk da ikirarin rundunar sojin Najeriya na karya lagon karfin Boko Haram, amma har yanzu kungiyar na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashi, inda a kwana rahotanni suka ce wasu mahara da ke tunanin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Katarko a jihar Yobe inda suka kori mutanen gari tare da kone gidaje.

Wasu Kekunan 'yan Boko Haram suka gudu suka bari

Asalin hoton, @HQNigerianArmy

Bayanan hoto, Wasu Kekunan 'yan Boko Haram suka gudu suka bari