ICRC: Mahaifin Hauwa na jimamin mutuwarta

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar mahaifin Hauwa da BBC:

Bayanan sautiMuryar mahaifin Hauwa Liman da Boko Haram suka kashe

Muhammed Liman, mahaifin ma'aikaciyar kungiyar bayar da agaji ta Red Cross, Hauwa Liman ya bayyana wa BBC irin halin bakin cikin da ya tsinci kansa a ciki lokacin da ya samu labarin rasuwar 'yarsa.

"Abun ya dame mu wallahi, gaba daya iyalinmu, duka mutanenmu da abokananmu duk muna jin damuwa sosai" a cewarsa.

Ya kuma bayyana 'yar tasa a matsayin mutumiyar kirki, wacce ta zauna lafiya da kowa a lokacin rayuwarta.

Ya ce "Ita mai kirki ce, kuma ba ta gaba da kowa."

An yi garkuwa da Hauwa da wasu sauran ma'aikatan agaji biyu a garin Rann da ke arewacin Najeriya.

Daya daga cikinsu ita ce Saifura Ahmed Khorsa wacce kungiyar Boko Haram din ta kashe a watan da ya gabata.

Garin Rann da ke Arewa maso gabashin Najeriya

Hauwa Liman da Saifura Khorsa na aikin kula da mutanen da suka rasa gidajensu a garin Rann da ke Jihar Borno, inda nan ne tashin hankali ya fi yawa lokacin da aka sace su a watan Maris.

Dayar wacce aka sace ita ce Alice Loksha, malamar jinya a wata cibiya da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ke tallafawa a lokacin da a ka sace ta.

An yi garkuwa ne da su lokacin da kungiyar ISIS reshen Afirka ta yamma ISWAP ta kai hari garin ran 1 ga Maris din wannan shekarar.

Wasu ma'aikatan agaji uku da jami'an tsaro takwas aka kashe a harin.

A watan da ya gabata ne ICRC ta sami bidiyon da ke nuna kisan Saifura Khorsa.

Hauwa Liman

Asalin hoton, ICRC

Bayanan hoto, Hauwa Liman na aiki ne a garin Rann lokacin da aka yi garkuwa da ita

Wata guda cif bayan kashe Saifura Khorsa, ranar Litinin, wani hoton bidiyo ya fito inda aka nuna kisan Hauwa Liman.

Wani dan jarida da ya ga bidiyon ya ce harbin ta aka yi.

Hukumar ICRC ta ce Hauwa "na da son mutane da kazar-kazar, wacce iyayenta da kawayenta ke matukar kauna.

"Ta na da mayar da hankali wajen aikinta na taimakon mata marassa galihu a unguwarsu," in ji hukumar.

Wannan layi ne

Buhari ya yi wa iyayenta ta'aziyya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa iyayen Hauwa ta'aziyya ta wayar sadarwa, inda ya tabbatar wa mahaifinta cewa gwamnati ta yi bakin kokarinta don ganin an ceto 'yarsa, sai dai yana bakin cikin rashin yiwuwar hakan.

Shugaban ya ce bai ji dadin yadda duk da kokarinta na taimakon al'umma amma Boko Haram suka yi mata kisan gilla ba.A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ya aike wa manema labarai, ya ce yana taya hukumar ICRC jimamin mutuwar ungozomar, tare da gode musu kan yadda suke ayyukan agaji a kasar.

Ya nemi ICRC da ka da ta gaza ko gwiwarsu ta yi sanyi wajen ci gaba da taimakon Najeriya, duk da rashin ma'aikatansu da suka yi.

Wannan layi ne

Me mayakan suka bukata?

Sharhi daga wakilin BBC Chris Ewokor

Mayakan dai ba su bayyana abun da suke bukata ba a sarari.

Amma sun bayyana cewa dalilinsu na kashe Saifura Khorsa a watan Satumba shi ne, sun mika wa gwamnatin Najeriya bukatunsu amma aka yi burus da su.

Gwamnatin dai ba ta bayyana abun da masu ikirarin jihadin suka nemi da a yi musu ba.

Babu wata alama da ke nuna dalilin da ya sa mayakan su ka sa wa kungiyar ICRC ido ganin cewa ita ta shiga tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram lokacin da aka sako 'yan matan Chibok a 2017.

A wata gajeruwar sanarwa da kungiyar ISWAP ta fitar bayan kisan Hauwa Liman, ta ce ta kashe ungozomomin ne saboda "sun watsar da addinin musulunci lokacin da suka zabi su yi aiki da kungiyar Red Cross".

Wannan layi ne

Wacece Hauwa Liman?

  • Shekararta 24
  • Ta yi aiki a matsayin Ungozoma da kungiyar bayar da agaji ta The International Committee of the Red Cross (ICRC)
  • Kungiyar ISIS reshen Afirka ta yamma ISWAP ta yi garkuwa da ita ran 1 ga watan Maris shekarar 2018
  • Kungiyar ta kashe ta ranar 15 ga Oktoba shekarar 2018
  • 'Yar asalin jihar Borno ce.
Wannan layi ne